Bakin Jinin APC Zai Shafe Ku ": Dan Takarar NNPP Ya Soki Masu Komawa Jam'iyyar
- Dan takarar gwamna a zaben jihar Ondo a jam'iyyar NNPP, Olugbenga Edema ya caccaki wadanda suka koma APC
- Edema ya ce ya tabbata sun jahilci yadda APC ta ke a Ondo da kuma kiyayya da yan jihar ke nuna mata a fili
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar a ranar 16 ga watan Nuwambar 2024 da muke ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Dan takarar gwamna a jihar Ondo karkashin jam'iyyar NNPP, Olugbenga Edema ya yi magana kan wadanda suka koma APC.
Edema ya caccaki wadanda suka sauya sheka zuwa APC inda ya ce sun tafka babban kuskure a siyasa.
Dan takarar NNPP a Ondo ya soki APC
'Dan takarar ya ce haka ya nuna cewa ba su san yadda jam'iyyar APC take ba a jihar Ondo, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Edema ya ce da sun sani kuwa da ba su shiga APC ba saboda jam'iyyar ba ta da dan takarar gwamna a zaben watan Nuwambar 2024.
Har ila yau, ya ce tsarin da aka bi wurin samar da Gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin zaɓaɓɓen dan takara ya saba ka'ida.
Ondo: Edema ya shawarci masu shiga APC
"Ya kamata su fahimci yadda al'umma suka ki jinin APC da kuma yadda aka yi zanga-zangar adawa da mulkin APC."
"Ubangiji da kansa ba ya tare da gwamnatin Aiyedatiwa saboda shi ba ya goyon bayan gurbatacciyar gwamnati."
- Olugbenga Edema
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar a ranar 16 ga watan Nuwambar 2024 na wannan shekara.
Mukarraban Mimiko sun sauya sheka zuwa APC
Kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo ta gamu da gagarumin koma baya yayin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamna a wannnan shekarar.
Abokan siyasa da makusantan tsohon gwamnan jihar, Olusegun Mimiko, da manyan jiga-jigai sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Waɗanda suka sauya shekar sun haɗa da tsohon ɗan majalisar tarayya, Hon Victor Akinjo da tsohon kakakin majalisar dokokin Ondo, Hon Joseph Akinlaja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng