Kananan Hukumomi: PDP Ta Fasa Shiga Zabe, Ta Jefi Jam'iyyar APC da Manyan Zargi
- Yayin da ake shirin gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Oktoban 2024 a Jigawa, jam'iyyar PDP ta janye shiga zaben
- Jam'iyyar ta zargi hukumar zaben jihar ta SIEC da tsauwalawa a kudin siyan fom na takara tare da zargin taya APC yin magudi
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam'iyyar a jihar, Hon. Ali Idris Diginsa ya fitar a ranar Larabar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Jigawa - Jam'iyyar PDP a jihar Jigawa ta janye shiga zaben da za a gudanar na kananan hukumomi a watan Oktoban 2024.
Jam'iyyar na zargin hukumar zaben jihar (SIEC) kan tsauwala farashi wurin siyar da fom na yan takarar kansila da ciyamomi.
PDP ta janye shiga zaben jihar Jigawa
Tribune ta ruwaito shugaban PDP a jihar, Hon. Ali Idris Diginsa na tabbatar da janyewarsu daga shiga zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Diginsa ya ce sun dauki matakin ne saboda tsabar kudi na takara har N5m na ciyaman da kuma N2m na kansila a zaben da za a yi.
Ya ce jam'iyyar ba ta gamsu da shirin hukumar zaben jihar ba wurin gudanar da shi cikin adalci ba tare da murdiya ga jam'iyyar APC ba.
Jam'iyyar ta yi mummunan zargi kan APC
"Jam'iyyar PDP ta yanke shawarar fita daga zaben da za a gudanar saboda kudin siyan fom din takara har N5m na ciyaman da kuma N2m na kansila."
"Shugaban hukumar zaben da mambobinsa duk 'yan jam'iyyar APC ne da suke shiga lamuran siyasarta wanda ya saba ka'idar kafa hukumar."
"Kudin fom din takara da aka sanya an yi ne domin hana yan jam'iyyun adawa tsayawa neman kujera a zaben duba da halin matsin tattalin arziki a yanzu."
- Ali Idris Diginsa
PDP ta kwace ikon Majalisar jihar Abia
Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi nasarar kwace ikon Majalisar jihar Abia bayan sake rantsar da 'dan majalisa a jiya Talata 13 ga watan Agustan 2024.
Rantsar da sabon 'dan majalisar ya biyo bayan hukuncin kotun zabe tun a watan Nuwambar 2023 da kakakin Majalisar ya ki bin umarnin kotun.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng