Kotu Ta Kori Korafin Yan Takarar APC da NNPP, Ta Fadi Wanda Ya Lashe Zaben Sanata
- Sanata Pam Mwadkon na jam'iyyar ADP ya yi nasara a kotun sauraran kararrakin zabe da ke zamanta a jihar Bauchi
- Sanata Pam ya samu nasara bayan korar korafe-korafen 'yan takarar jam'iyyun APC da kuma NNPP a shari'ar
- Wannan na zuwa ne bayan yan takarar sun shigar da korafi kan nasarar Mwadkon a watan Faburairun 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Kotun sauraran kararrakin zabe ta yi zama kan korafin zaben cike gurbin Sanata da aka gudanar.
Kotun ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar ADP, Pam Mwadkon Dachungyang a matsayin wanda ya lashe zaben a mazabar Plateau ta Arewa.
Plateau: Kotu ta raba gardama kan zabe
Alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a, Cordelia Ogadi sun yi fatali da korafin 'yan takarar jam'iyyun APC da NNPP, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan takarar da aka kori kararsu sun hada da na NNPP, Shafi'u Sahlan da kuma na APC, Chris Giwa saboda rashin hujjoji.
Wannan hukunci ya tabbatar da matakin da hukumar INEC ta dauka bayan sanar da Mwadkon a matsayin wanda ya yi nasara a zaben watan Faburairun 2024.
Sanata Dachungyang ya yi martani kan nasararsa
Yayin da ya ke martani, Sanata Mwadkon ya ce hukuncin ya tabbatar da goyon baya da yan mazabarsa suka ba shi.
Hadimin sanatan a bangaren yada labarai, Eric Dung shi ya bayyana haka a yau Laraba 14 ga watan Agustan 2024.
Sanatan ya ce ya san dawainiyar da yake kan kujerar sanata inda ya yi alkawarin cire musu kitse a wuta.
Enugu: Kotu ta tsige dan Majalisar PDP
Kun ji cewa Kotun sauraron korafe-korafen zabe ta tsige dan Majalisar Wakilan Tarayya mai wakiltar mazaɓar Igboeze ta Arewa/Udenu Hon. Simon Atigwe.
Kotun zaben ta kuma bayyana dan takarar jam'iyyar LP, Dennis Nnamdi Agbo a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben dan Majalisar Igboeze.
Tun farko dai dan takarar LP ne ya samu nasara a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, amma Kotun Daukaka Kara ta sauke shi, ta ba da umarnin sake zabe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng