Tallafin Tinubu: Abba Kabir Ya Fusata da Zargin APC, Ya Fadi Yadda Aka yi a Kano
- Gwamnatin Abba Kabir na jihar Kano ta caccaki jam'iyyar APC kan zargin yin kwana da kayan tallafin Gwamnatin Tarayya
- Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Shehu Bala Sagagi ya bayyana zargin a matsayin bita-da-kullin siyasa domin bata suna
- Wannan na zuwa ne bayan zargin da APC ta yi a jihar kan wawushe kayan tallafin abinci da Gwamnatin Tarayya ta bayar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi magana kan zargin handame tallafin abinci na Gwamnatin Tarayya da APC ta yi.
Gwamnatin ta ƙaryata zargin inda ta ce APC na neman batawa Gwamna Abba Kabir suna ne da kuma bita-da-kullin siyasa.
Tallafin: Abba ya yi martani ga APC
Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Shehu Bala Sagagi shi ya yi martanin a yau Laraba 14 ga watan Agustan 2024, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sagagi ya ce wannan wata makarkashiya ce da APC ta shirya domin bata sunan Abba Kabir a kokarin da yake yi na taimakawa al'ummar Kano.
Shugaban ma'aikatan ya ce zargin APC ba shi da tushe bare makama kuma an yi ne domin siyasa kawai, Daily Post ta tattaro.
Abba ya fadi yadda yake rabon tallafi
"Bari in sanar da ku ofishina bai karbi wani kayan tallafi domin rabawa ga jiha ko kuma kananan hukumomi ba."
"Gwamnatin NNPP tana raba kayan tallafi cikin gaskiya inda kowa ya san a bayyana yake akwai bayanai kan wadanda suka karba da yadda aka yi rabon."
"Babu kamshin gaskiya kan zargin da jam'iyyar APC ke yi game da rabon tallafin."
- Shehu Bala Sagagi
Kano-APC tana zargin an karkatar da tallafi
Kun ji cewa Jam’iyyar APC ta buƙaci a gudanar da bincike kan zargin karkatar da shinkafar da Gwamnatin Tarayya a Kano.
Jam’iyyar ta kuma buƙaci da a gaggauta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kwamitin bincike mai zaman kansa.
Hakan ya biyo bayan ba da tallafin abinci ga jihohin Najeriya baki daya da Gwamnatin Tarayya ta yi saboda halin kunci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng