Sanata Daga Arewa Ya Yi Nasara a Kotun Ɗaukaka Ƙara, Ya Tabbata Cikakken Ɗan APC
- Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da Sanata Muhammad Ɗanjuma Goje a matsayin halastaccen mamban jam'iyyar APC
- Alkalai uku da suka saurari ƙarar da sanatan ya shigar sun jingine hukuncin babbar kotun tarayya wadda ta tabbatar da korarsa daga APC
- Tun farko dai APC a gundumar Kashere da ke jihar Gombe ta kori Ɗanjuma Goje bisa zargin cin amana, matakin da ya nuna bai gamsu da shi ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Gombe - Kotun daukaka kara mai zama a Abuja, ranar Talata, ta tabbatar da Sanata Muhammad Danjuma Goje a matsayin halastaccen ɗan jam'iyyar APC a jihar Gombe.
Alƙalai uku da suka ƙunshi mai shari'a Abba B. Mohammed, Mai Shari'a E.O. Abang da Mai Shari'a P.C. Obiora ne suka yanke wannan hukuncin da murya ɗaya.
Goje: Alkalai sun soke hukuncin karamar kotu
Alkalan sun jingine hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke, wanda ta hana Sanata Goje bayyana kansa a matsayin mamban APC, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun farko dai shugabannin APC na gundumar Kashere, ƙaramar hukumar Akko ta jihar Gombe ne suka kori Sanata Ɗanjuma Goje daga jam'iyyar, kuma kotun ta tabbatar.
A watan Yuli 2023 ne Sanata Goje ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na tabbatar da korarsa daga APC, rahoton The Cable.
Sanata Danjuma Goje ya ɗaukaka ƙara
A ranar 4 ga Yuli, 2023 Ɗanjuma Goje ta hannun lauyansa, Paul Erokoro (SAN), ya shigar da kara gaban kotu yana kalubalantar korar da aka masa daga jam’iyyar.
Ya shaida wa kotun cewa ƙaramar kotu ta yi kuskure a cikin hukuncin da ta yanke, saboda an take masa haƙƙi kuma ba a saurari hujjojinsa ba.
A cewar Ɗanjuma Goje, shugaban APC na gundumar, Tanimu Abdullahi bai faɗi laifin da ya aikata ba wanda ya sa aka fitar da shi daga APC.
Kotu ta ci tarar jam'iyyar APC
A halin yanzu, kotun ɗaukaka ƙara ta jingine hukuncin babbar kotun tarayya kuma ta tabbatar da Sanata Ɗanjuma Goje a matsayin halastaccen ɗan APC.
Alkalan kotun sun yi watsi da hukuncin, sannan suka umarci APC reshen jihar Gombe ta biya tarar N200,000.
Gwamna ya ƙara lallaɓa matasa
A wani rahoton kuma gwamnan jihar Benuwai ya yi kira da roƙo ga matasa su daina shiga ayyukan laifi, su rungumi zaman lafiya don samun ci gaba.
Mai girma Hyacinth Alia ya bayyana cewa duk wani ƙoƙari da gwamnati ke yi don gyara goben matasa ne, don haka ya roki su kama hanya mai ɓullewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng