Jerin Na Jikin Buhari da Tinubu Ya Yi Wa Kara da Ruwan Mukamai a Cikin Mako 1
Gwamnatin jihar Katsina ta yabawa Shugaba Bola Tinubu kan nadin 'yan jihar Katsina mukamai daban-daban.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Mukaddashin gwamnan jihar, Faruq Jobe ya yabawa shugaban wurin ba 'yan jihar mukaman da kuma ganin dacewarsu.
Gwamnatin ta bayyana nadin tsohon Gwamna, Aminu Bello Masari da wasu mutane uku daga jihar da cewa abin alfahari ne.
Legit Hausa ta binciko muku wadanda aka ba mukaman daga Katsina:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Aminu Bello Masari
Bola Tinubu ya nada Aminu Bello Masari a matsayin shugaban hukumar tallafin ilimi ta TETFund.
A matsayinsa na shugaban hukumar, Masari zai kula da inganta makarantun gaba da sakandare wurin ba su tallafi da goyon baya.
Masari tsohon gwamnan jihar Katsina ne daga shekarar 2015 zuwa 2023 kafin Gwamna Umaru Dikko Radda ya karbi madafun iko.
2. Kabir Ibrahim Mashi
Ibrahim Mashi a bangarensa, ya samu mukamin kwamishinan Gwamnatin Tarayya a hukumar rarraba kudaden shiga ta RMAFC.
Mashi zai kula da hukumar domin tattabar da rabon kudin a tsakanin Gwamnatin Tarayya da kananan hukumomi da jihohi.
3. Abdullahi Alhassan Imam
Har ila yau, daga jihar Katsina, Bola Tinubu ya nada Abdullahi Imam a matsayin shugaban hukumar kula da hada-hadar kudi ta NCTO.
Tinubu ya nada Imam ne domin inganta tare da tabbatar da tsarin hukumar NSIPA da ke jagorantar tsarin CCT.
4. Badamasi Lawal Charanchi
Bola Tinubu ya ba Lawal Charanchi mukami a matsayin babban daraktan hukumar NSIPA da ke ragewa al'umma radadin talauci.
Hukumar NSIPA ta na karkashin ma'aikatar jin kai da suka hada tsarin CCT da ciyar da daliban makaranta da kuma N-Power.
5. Labiru Musa Kafur
Har ila yau, hadimin Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale ya sanar da nadin Labiru Musa Kafur daga jihar Katsina.
Kafur wanda ya sakataren din-din-din a gwamnatin Katsina fiye da shekaru 10 ya samu mukamin shugaban kwamitin gudanarwa na cibiyar harshen Faransanci a Najeriya a Lagos.
Tinubu ya sallami na hannun daman Buhari
A wani labarin mai kama da wannan, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sallami shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa.
Tinubu ya kori Mohammed Bello-Koko a matsayin babban daraktan hukumar wanda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada lokacin mulkinsa.
Tinubu ya maye gurbin Bello-Koko da Abubakar Dantsoho wanda zai shafe shekaru biyar a matsayin shugaban hukumar a Najeriya.
Asali: Legit.ng