2027: Tsohon Shugaba a APC ya Fara Yunkurin Doke Tinubu, Ya Tabo Atiku da Kwankwaso

2027: Tsohon Shugaba a APC ya Fara Yunkurin Doke Tinubu, Ya Tabo Atiku da Kwankwaso

  • Tsohon shugaba a jam'iyyar APC mai mulki, Lukman Salihu ya yi kira na musamman ga jam'iyyun adawa a Najeriya
  • Lukman Salihu ya bukaci yan adawa su yi amfani da halin da ake ciki a Najeriya damin fara kokarin kwace mulki a 2027
  • Haka zalika ya bukaci yan APC da ya ce an yi biris da su a tafiyar, su hada kai da yan adawa domin kawo sauyin gwamnati

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin APC na kasa a yankin Arewa ta yamma, Lukman Salihu ya yi kira na musamman ga yan jam'iyyun adawa.

Lukman Salihu ya bukaci Atiku Abubakar, Rabi'u Kwankwaso da Peter Obi su hada kai domin kawo karshen mulkin APC a Najeriya.

Kara karanta wannan

Taraba: Kungiyar CAN ta ba da umarnin yin addu'o'i da azumi na kwanaki 3

Salihu Lukman
Tsohon jigon APC ya fara neman kayar da Tinubu a 2027. Hoto: @officialAPCng
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Lukman Salihu ya yi kira ga Yemi Osinbajo da sauran yan APC kan shiga jam'iyyar adawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran Lukman ga Atiku, Kwankwaso da Obi

Lukman Salihu ya yi kira na musamman ga manyan jagororin jam'iyyun adawa a Najeriya kan su hada jam'iyya daya domin samun nasara a zaben 2027.

'Dan siyasar ya ce idan Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabi'u Kwankwaso suka gaza hada kai ba lallai su iya kawo karshen mulkin Bola Tinubu ba a 2027.

Sako zuwa ga shanun waren APC

A daya bangaren, Salihu ya yi kira ga tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi da su koma jam'iyyar adawa.

A cewar Lukman Salihu, APC ta yi biris da su a cikin tafiyarta saboda haka ya kamata su koma cikin yan adawa domin ceto Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon PDP ya fadi yadda Tinubu zai magance matsalolin Najeriya

Lukman ya yi maganar zanga zanga

Jaridar the Sun ta wallafa cewa Lukman Salihu ya ce bayan zanga zanga da aka yi alamu sun nuna shugaba Bola Tinubu ba shi da wata hanya ta magance matsalolin Najeriya.

Saboda haka ya bukaci yan adawa su yi amfani da damar domin samun hadin kan yan Najeriya wajen kayar da APC a 2027.

Manyan Arewa sun yi martani ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yi jawabi ga yan kasa kan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da aka yi a Najeriya.

Kalaman da Bola Tinubu ya yi sun tayar da kura inda mutane da dama suka masa martani mai zafi daga sassa daban daban ciki har da manyan Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng