Ana Cikin Kushe Mulkin APC, Ɗan Takarar Shugaban Kasa a PDP Ya Dawo Jami'yyar
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Dakta Cosmos Ndukwe ya sauya sheka zuwa jami'yyar APC
- Ndukwe kafin komawa APC ya rike mukamai da dama a jihar ciki har da shugaban ma'aikata da kuma kwamishina lokuta da dama
- Mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu shi ya karbi sabon tuban a karamar hukumar Bende da ke jihar Abia
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Abia - Jam'iyyar APC ta yi babban kamu bayan tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP ya watsar da jami'yyarsa.
Mataimakin shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Benjamin Kalu shi ya karbi tsohon dan takarar mai suna Dakta Cosmos Ndukwe.
An karbi dan takarar shugaban kasa a APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Kalu, Levinus Nwabughiogu ya fitar, cewar Tribune.
Kalu ya karbi sabbin tuban ne a yankin Awuja da ke karamar hukumar Bende da ke jihar Abia, The Nation ta tattaro.
Kalu ya yi masa alkawarin daidaito a jam'iyyar APC inda ya ce Bola Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da kawo sauyi a Najeriya a halin yanzu.
Mukaman da Ndukwe ya rike kafin zuwa APC
Ndukwe kafin komawa jam'iyyar APC ya riƙe muƙaman siyasa da dama a PDP da suka haɗa da kwamishina a jihar a lokuta dama.
Ya kuma rike mataimakin kakakin Majalisar jihar da mataimakin shugaban karamar hukumar Aba ta Arewa da kuma kansila a jihar.
Sannan ya rike mukamin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar a mulkin tsohon gwamna T A Orji da sauran mukamai daban-daban.
Mataimakin gwamnan Edo, Shaibu ya dawo APC
Kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya dawo jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya kwana ɗaya bayan kai masa farmaki.
Shaibu kafin dawowa APC ya bayyana cewa ruhinsa yana jam'iyyar kawai dai shi ne bai shigo ta ba amma ya kusa sauya sheka.
Mataimakin gwamnan jihar yana takun-saka da Gwamna Godwin Obaseki tuntuni wanda har ya jawo aka tsige shi a mukaminsa.
Asali: Legit.ng