Ganduje Ya Yi Babban Kamu a APC Bayan Sauya Shekar Mataimakin Gwamna

Ganduje Ya Yi Babban Kamu a APC Bayan Sauya Shekar Mataimakin Gwamna

  • Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje ya karbi mataimakin gwamnan jihar Edo zuwa jam'iyyar APC
  • Ganduje ya karbi Philip Shaibu bayan ya watsar da jam'iyyar PDP kwanaki uku bayan dawo da shi kan mukaminsa
  • Wannan na zuwa ne bayan kai wa Shaibu mummunan hari bayan hukuncin kotu da ya dawo da shi kujerarsa bayan tsige shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya watsar da jam'iyyar PDP a jihar.

Shaibu wanda kotu ta dawo da shi kan mukaminsa bayan tsige shi ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Mataimakin gwamnan PDP ya koma APC, Ganduje ya karbe shi
Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya sauya sheka zuwa APC inda Ganduje ya karbe shi a jihar. Hoto: Philip Shaibu.
Asali: Facebook

Edo: Gandue ya karbi Shaibu zuwa APC

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fara zawarcin mataimakin gwamnan PDP, za ta kafa tuta a ofishinsa

Mataimakin gwamnan ya koma APC ne yayin kaddamar da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar saboda zaben jihar, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da ganawar a yau Asabar 20 ga watan Yulin 2024 wanda ya samu halartar shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa da na Cross River, Bassey Otu, Punch ta tattaro.

Sai kuma shugaban jam'iyyar APC a jihar, Jarett Tenebe da dan takarar gwamnan jihar, Monday Okpebholo da Sanata Adams Oshiomole.

Ana zargin PDP da kaiwa Shaibu hari

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan wani mummunan hari da wasu miyagu suka kai wa Shaibu ana tsaka da murnar hukuncin kotu.

Harin ya jawo kace-nace da zarge-zarge inda APC ta zargi PDP ta kisa harin saboda dawo da Shaibu mukaminsa.

APC tana zawarcin Philip Shaibu a Edo

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban PDP ya fusata da yadda wasu ke 'satar' kudi, ya fice daga jam'iyyar

Kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ci gaba zawarcin mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu.

Shugaban APC reshen jihar Edo, Jarrett Tenebe ya yi kira ga Kwamared Shaibu ya jefar da ƙwallon mangwaro ko ya huta da ƙuda kana ya dawo cikin APC.

Tenebe, wanda ya samu rakiyar wasu kusoshin APC, ya bayyana harin da aka kaiwa Shaibu a filin jirgin sama a matsayin yunƙuri na ɗaukar rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.