Za a Fito da Wani Salon Zanga Zanga, ‘Yan Majalisar Kano Za Su Shiga Barazanar Farko

Za a Fito da Wani Salon Zanga Zanga, ‘Yan Majalisar Kano Za Su Shiga Barazanar Farko

  • An fara kawo shawarar ayi kiranye ga duk sanata ko ‘dan majalisar wakilan da ba gamsu da wakilcinsa ba
  • Mubakar Lawal Ibrahim wanda malami ne kuma ‘dan kasuwa a jihar Kano ya kawo wannan shawarar a yanzu
  • Burin Malam Mubakar Lawal Ibrahim shi ne ‘yan majalisa su fadawa shugaban kasa abin da talakawa suke so

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Babu mamaki nan gaba kadan a ji labarin cewa za ayi kiranye a tsige ‘yan majalisar wakilan tarayya da sanatocin kasar nan.

Ganin yadda zanga-zangar lumana ta dauki salon ta’adi da tada tarzoma, wasu sun fara bijiro da sababbin dabarun da za a kawo gyara.

'Yan majalisa
Zanga-zanga: Ana kawo shawarar yi wa 'yan majalisar Kano kiranye Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Za a maido 'yan majalisar Kano gida?

Kara karanta wannan

An samu babbar matsala: 'Yan sanda sun ba masu zanga-zanga shawari mai daukar hankali

Malam Mubakar Lawal Ibrahim ya dauko jan aiki, yana yin kira ga jama’a a Facebook cewa a fara waiwayen ‘yan majalisar tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, za su nemi ‘yan majalisar da suka zaba su dawo gida idan har ba za su iya kare muradun jama’a a birnin tarayya ba.

Zanga-zanga za ta iya dawowa kiranye

“Zanga-zangarmu za ta canja salo jama'a zuwa kiranyen sanatoci da ƴan majalisa, ko su nema mana abinda mu ke so kaɗai!”

Mubakar Lawal Ibrahim ya ce manufarsu ita ce ‘yan majalisar wakilai da sanatocin da ke majalisar dattawa su kawo masu mafita.

Daga cikin wadanda yake so su taya shi wannan aiki akwai fitaccen lauyan nan Abba Hikima da ‘dan gwagwarmaya, Kabir Dakata.

Kamar Abba Hikima ya goyi bayan shirin, ya ce duk 'dan majalisar da bai yakar manufofin gwamnati, bai da amfani ga mazabarsa.

Kara karanta wannan

Yadda zanga zangar lumana ta zama silar barna da lalata dukiyoyin miliyoyi a Kano

Abin da ake so daga 'yan majalisar Kano

“Bu mu bukatar komai. A dawo da tallafin man fetur.”
“Duk yadda za a yi, a samar da tsaro a Katsina, Zamfara da duka sauran jihohi.”

Mubarak Mudi Sipikin ‘dan siyasa ne, ya bayyana cewa tun ba yau ba ya dade yana irin wannan kira, amma ba a saurare shi ba.

Jama'a sun karbi shawarar kiran 'yan majalisa

Matashin ‘dan siyasar ya yi magana a shafinsa, mutane kuwa su na ta na'am da hakan.

Legit ta lura mutane da-dama sun yi na’am da lamarin, su na ganin hakan zai fi tasiri a kan a fita titi da sunan zanga-zangar lumana.

Babu ruwan Tinubu, laifin 'yan majalisa ne

An ga Sheikh Salihu A. A Imam a wani fai-fai da yake yawo a Facebook, ya na irin wannan kira a wata huduba da ya gabatar a masallaci.

Limamin ya ce babu bukatar a zagi Bola Tinubu, ‘yan majalisa suke da ikon taka masa burki amma sun ci amanar wadanda suke wakilta.

Kara karanta wannan

"Jami'an tsaro sun gano sanata mai daukar nauyin zanga zanga," Minista Wike ya yi magana

Ana da labarin cewa wasu bata-gari sun yi barna sosai a garin Kano, an fasa shagon har da wani mai goyon bayan zanga-zangar lumana.

Matsin rayuwa da aka shiga ya jawo dole mutane su ka hau titi, a karshe miyagu su ka buge da yin barna bayan malamai sun ja kunne a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng