“Mota 1 Kacal Na Ke da Shi”: Minista Atiku Bagudu Ya Fadi Yawan Albashinsa

“Mota 1 Kacal Na Ke da Shi”: Minista Atiku Bagudu Ya Fadi Yawan Albashinsa

  • Yayin da 'yan Najeriya ke yawan korafi kan albashi da alawus na mukarraban gwamnati, Minista ya fayyace gaskiya
  • Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya bayyana cewa kwata-kwata albashinsa bai kai ko miliyan daya ba
  • Yayin da ya yake maganar alawus, Bagudu ya ce bai san wani takamaimai alawus da Minista ke samu ba ban da albashi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya yi magana kan zargin facaka da suke yi a gwamnati.

Bagudu ya ce kwata-kwata mota daya yake shiga a hukumance inda ya bayyana cewa albashinsa ko miliyan daya bai kai ba.

Bagudu ya fadi yawan albashinsa a matsayin Minista
Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya yi magana kan albashinsa. Hoto: Sen. Abubakar Atiku Bagudu.
Asali: Facebook

Bagudu ya fadi yawan albashinsa na Minista

Kara karanta wannan

Dalilin shigata zanga zangar lumana a Kano Inji tsoho mai shekaru kusan 70 a suniya

Ministan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Asabar 3 ga watan Agustan 2024 a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan Kebbi ya ce bai san da wani alawus da Minista ke karba ba idan ba albashinsa ba da ya ke samu ba.

Ya ce kashe kudi a gwamnati ya yi yawa amma kudin da Minista ke samu hukumar rarraba kudi ta RMAFC ke kayyadewa.

Minista Bagudu ya yi magana kan alawus

"Wani lokaci ko kuma mafi yawan Ministoci kamar ni misali mota daya na ke da shi daga ofis wanda ba na ma amfani da ita."
"Mafi yawan lokuta ina amfani da motata kirar 'Camry" saboda ina son nuna shugabanci a matsayina na Ministan kasafi."
"Maganar yadda ake biyan Minista kuma bai kai ma N1m ba kuma ban san wani alawus da muke samu ba."

Kara karanta wannan

Bayan gwamna a Arewa ya ki albashin N70,000, NLC ta fadi matakin da za ta dauka

- Atiku Bagudu

Bagudu ya ce bai san da maganar wani alawus ba kuma zai iya yada albashinsa kowa ya gani saboda a bayyane ya ke.

Bagudu ya yabawa tsare-tsaren Tinubu

Kun ji cewa Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya yabawa matakan da Bola Tinubu ya dauka a Najeriya.

Bagudu ya ce matakin cire tallafin mai da Tinubu ya yi, ya aiwatar da abin da ya kamata a yi shekaru da dama da suka wuce.

Tsohon dan Majalisar Tarayya ya ce abin da sauran shugabanni da 'yan takara suke son yi ne suka gagara Tinubu ya aiwatar a lokaci guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.