Fadar Shugaban Ƙasa Ta Faɗi Wasu Manyan Kusoshin Gwamnati da Hannu a Zanga Zanga
- Fadar shugaban ƙasa ta zargi wasu masu karfin faɗa a ji a gwamnati da hannu a shirya zanga-zangar da za a fara yau Alhamis
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin ɗalibai, Sunday Asefon ne ya bayyana hakan a wani taro da aka shirya a Abuja
- Ya ce masu ƙarfin faɗa ajin da wasu makiyan Najeriya suka shirya saboda suna baƙin ciki da nasarorin Shugaba Tinubu a shekara ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta yi zargin cewa wasu manya masu ƙarfin iko a gwamnati da maƙiyan Najeriya ne suka haɗa wannan zanga-zangar da za a fara yau Alhamis.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin dalibai, Sunday Asefon, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja a taron da aka shirya kan zanga-zangar.
Shugaban Otal ɗin Wells Carlton Hotel and Apartments, Mista Osahon Okunbo ne ya shirya taron, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fadar shugaban ƙasa ta tona masu hannu
A cewar Asefon, masu karfin faɗa a ji da ake kira 'cabals' da wasu gurɓatattu na da hannu a wannan yunkuri na zanga-zanga domin suna jin haushin ci gaban da gwamnatin Tinubu ke samu ba.
Ya ce:
"Sun saba da tsarin da ake nada ministoci bisa la’akari da yawan shekaru, amma Shugaba Tinubu ya zo ya canza hakan.
"Shugaban ƙasa ya kawo matasa kuma ya bullo da manufofin da ba su dace da muradansu ba.”
Bola Tinubu ya kafa tarihi
Sunday Asefon ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin Bola Tinubu ta samu musamman a fannin ilimi
"Babu wani shugaban kasa da ya cimma abin da Shugaba Tinubu ya yi a cikin shekara guda."
"Shugaba Tinubu ya tabbatar da tsarin lamunin dalibai ya zama gaskiya, ya warware matsalar da ta dade tsakanin gwamnatin tarayya da malaman jami'o'i. Ya bullo da tsare-tsare masu amfani ga matasa.”
Asefon ya koka kan yadda ya gaza bayyana nasarorin da Tinubu ya samu ga al'umma yadda ya kamata, musamman a jami’o’in Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya yi iƙirarin cewa babu wasu masu ƙarfin faɗa aji da ke juya akalar gwamnatinsa, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Sarkin Ife ya magantu kan zanga-zanga
A wani rahoton, an ji wani Sarkin yarbawa ya yi kira ga masu shirin yin zanga-zanga kan tsaɗar rayuwa su yi haƙuri su karawa Bola Tinubu lokaci.
Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya ce wahalhalu da tsadar rayuwar da mutane ke kuka a kai, al'amari ne da ya shafi duk duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng