Duk da Rigima Kan Sahihancinsa a Jam’iyyar, APC Ta Ba Yaron Wike Mukami
- Ministan Abuja, Nyesom Wike na cigaba da mamayar APC yayin da aka nada na hannun damansa mukami a jam'iyyar
- Jam'iyyar ta nada Ojukaye Flag-Amachree daga cikin mambobin kwamitin zaben jihar Edo da ake shirin yi a watan Satumba
- Wannan nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gudanarwa na jam'iyyar, Sulaiman Muhammad Argungu ya fitar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta ba na hannun daman Ministan Abuja, Nyesom Wike mukami a kwamitin kamfe na zabe.
Jam'iyyar ta nada Ojukaye Flag-Amachree a matsayin mamban kwamitin kamfe na zaben jihar Edo da ke tafe.
Jam'iyyar APC ta nada yaron Wike mukami
Sakataren gudanarwa na jam'iyyar, Sulaiman Muhammad Argungu shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Argungu ya yaba da irin jajircewar Flag-Amachree ga jam'iyyar duba da irin gwagwarmayar da ya yi wurin cigaban jam'iyyar.
Wannan nadin na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a watan Satumbar 2024, Pulse ta tattaro.
APC ta shawarci Flag-Amachree kan aiki tukuru
"Wannan nadin naka a kwamitin zaben ya biyo bayan jajircewa da kake da shi da kuma nuna kwarewa a siyasa na tsawon shekaru."
"A matsayin mamban kwamitin zaben jihar Edo, ana bukatar ka yi amfani da duka kwarewarka a siyasa da sauran lamura domin tabbatar da nasarar dan takararmu a zabe."
- Sulaiman Muhammad Argungu
Wannan nadin na zuwa ne kasa mako daya bayan shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya kafa kwamitin kamfen a ranar 20 ga watan Yulin 2024.
Wike ya caccaki masu daukar nauyin zanga-zanga
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike a ranar Talata, 23 ga watan Yulin 2024 ya nuna rashin jin dadinsa game da shirin gudanar da zanga-zanga.
Wike ya bayyana zanga-zangar da aka shirya yi a watan Agustan shekarar 2024 a matsayin wacce za a yi saboda siyasa domin biyan buƙatar wasu tsiraru.
Asali: Legit.ng