An Gano Kuskuren da Zai Jefa Abba a Matsala a Kano, Hadimin Buhari Ya Ba Shi Mafita

An Gano Kuskuren da Zai Jefa Abba a Matsala a Kano, Hadimin Buhari Ya Ba Shi Mafita

  • Jami'in tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi kira na musamman ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
  • Bashir Ahmad ya bayyana kuskuren da Abba Kabir Yusuf yake yi wajen gudanar da ayyuka a jihar Kano tare da faɗin mafita a garesa
  • Duk da haka, matashin 'dan siyasar ya yabi Mai girma Abba Kabir bisa wasu muhimman ayyukan cigaba da ya kawo a jihar zuwa yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jami'in tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hanyoyin da gwaman Kano, Abba Kabir Yusuf zai bi domin kawo cigaba.

Bashir Ahmad ya ce duk da Abba Kabir Yusuf ya na kokari amma akwai abubuwan da ya kamata ya mayar da hankali a kansu a yanzu.

Kara karanta wannan

Abba Kabir ya kaddamar da muhimmin aikin da zai inganta yanayi da noma a Kano

Abba Kabir
An shawarci Abba Kabir kan ayyukan da ya kamata ya yi. Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Bashir Ahmad ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayyukan da Abba yake yi a yanzu

Bashir Ahmad ya bayyana cewa akwai abin burgewa kan yadda ayyuka da Abba yake suke tafiya cikin sauri.

Sai dai Bashir ya ce manyan gadoji da gwamnan yake yi ba su ne jihar Kano ta fi bukata ba a halin da ake ciki.

Bashir: 'Hanyoyi sun lalace a Kano'

Bashir Ahmad ya bayyana cewa a yanzu haka hanyoyin cikin Kano sun lalace wanda ya kamata gwamnati ta mayar da hankali a kansu.

Ya ce idan aka gyara hanyoyin harkar sufuri za ta inganta a Kano da za kuma a saukaka lamura a jihar.

Matsalar wahalar ruwa a jihar Kano

Har ila yau Bashir Ahmad ya bayyana cewa mutanen Kano na fama da matsalar rashin ruwan sha mai tsanani.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, tsohon kakakin kamfen Atiku ya fice daga PDP zuwa APC

A karkashin haka ya yi kira ga gwamna Abba Kabir Yusuf kan mayar da hankali wajen tabbatar da cewa mutane sun samu ruwa mai tsafta.

Haka zalika Bashir ya bayyana cewa jihar Kano ta cika da datti ta ko ina saboda haka ya bukaci gwamnan ya yi duba kan lamarin.

Abba ya dasa bishiyoyi a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin dasa miliyoyin bishiyoyi a fadin jihar.

Abba Kabir Yusuf ya fadi dalilin fara dasa bishiyoyin da amfanin da al'umma za su samu daga aikin dasa itacen a shekaru masu zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng