Bayan Ganawa da Tinubu, Tsohon Kakakin Kamfen Atiku Ya Fice Daga PDP Zuwa APC

Bayan Ganawa da Tinubu, Tsohon Kakakin Kamfen Atiku Ya Fice Daga PDP Zuwa APC

  • Daga karshe Daniel Bwala, tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen Atiku Abubakar ya bar jam'iyyar PDP
  • Bwala ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa Bola Tinubu a Aso Villa, ya sanar da komawa APC
  • Ya kara jaddada goyon bayansa ga gwamnatin Tinubu, inda ya ce nan ba da jimawa ba zai tabbatar da komawa gida watau APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon kakakin kwamitin yakin neman zaɓen Atiku Abubakar a zaɓen 2023, Daniel Bwala ya sanar da ficewa daga PDP zuwa APC mai mulki.

Bwala ya bayyana hakan ne yayin hira da ƴan jarida a fadar shugaban ƙasa jim kaɗan bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ranar Laraba, 24 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin kamfen PDP ya mayar da zazzafan martani ga Atiku kan zanga zanga

Daniel Bwala da Bola Tinubu.
Daniel Bwala ya tabbatar da sauya sheka daga PDP zuwa APC Hoto: Daniel Bwala
Asali: Twitter

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Daniel Bwala ya ce a halin yanzun yana tare da mai girma shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daniel Bwala ya bar PDP a hukumance

"Na baro PDP a hukumance kuma ina dab da shiga jam'iyyar APC, burina kamar na mutumin da ke shirin yin aure ne, ba zai yiwu ka wayi gari kawai ka kama hanyar coci ba.
"Dole sai ka harhaɗo abokai, ka sanar da ƴan uwa da abokan arziki domin su halarci wurin, su sa maka albarka. To kamar haka ne, ina hanyar komawa APC kuma dama nan ne gidanmu."
"Idan ba ku manta ba shekaru takwas na shafe a APC, kuma ina da tabbacin ku ƴan jarida kun san irin ƙoƙarin da muka yi da goyon bayan da muka bayar a APC.

- Daniel Bwala.

Meyasa Bwala ya bar APC a baya?

Kara karanta wannan

Tinubu: Fitaccen Sarki ya aika muhimmin saƙo ga matasa masu shirin yin zanga zanga

Bwala ya ƙara da cewa tun farko ya bar APC ne saboda saɓanin fahimta kuma yanzu ya dawo a lokacin da ake bukatar haɗin kai domin ciyar da ƙasar gaba, Channels tv ta rahoto.

Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu ya shirya sadaukar da kansa ga Bola Tinubu kuma nan ba da jimawa ba zai sanar da dawowa APC a hukumance.

Kwamishina ta ajiye aiki a Abia

Kuna da labarin Kwamishinar lafiya ta jihar Abia, Dr. Ngozi Okoronkwo ta miƙawa Gwamna Alex Otti takardar murabus daga muƙaminta.

Misis Okoronkwo ta yi murabus ne bayan dakatar da ita daga aiki bisa wasu zarge-zarge wanda aka kafa kwamiti domin gudanar da bincike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262