Kiranye: Dino Melaye ya mayar da martani daga gadon asibiti, ya yi godiya
A yau ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar da sakamakon tantance saka hannun jama'ar mazabar Kogi ta yamma dake bukatar a yiwa Sanata Dino Melaye kiranye.
A sakamakon da hukumar zabe ta saki da safiyar yau, Lahadi, ta bayyana cewar saka hannun mutane 18,762 kawai ta iya tantancewa daga cikin saka hannu 39,285 da ta karba domin tantancewa, hakan ya nuna cewar adadin masu bukatar a dawo da Sanatan ya gaza kai wa kaso 51% da doka ta bukata.
A wani sako da ya fitar ta bakin mai taimaka masa a bangaren yada, Mista Gideon Ayodele, Dino Melaye, ya mika sakon godiya ga jama'ar mazabar sa bisa kunyar da suka bawa abokan gamayyar sa.
Kazalika, Melaye, ya saki sakon godiya ga jama'ar mazabar sa a shafin sa na Tuwita tare da bayyana cewar babu yadda makiyan sa zasu iya da shi tunda Allah na tare da shi.
DUBA WANNAN: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani dangane da ziyarar Buhari a Amurka
Melaye ya mika godiya ta musamman ga kafafen yada labarai, masu saka ido, kungiyoyi da suka saka ido domin tabbatar da cewar ba a yi wuruwuru yayin tantance saka hannun jama'a ba.
Sanata Melaye, da yanzu haka ke kwance a babban asibitin Abuja inda yake samun kulawa bayan ya samu rauni a yayin da ya yi kokarin guduwa daga hannun 'yan sanda, ya bukaci jama'ar mazabar sa da magoya baya da su guji yin duk wani abu da iya zama matsala ga dokar kasa ko barazana ga zaman lafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng