Gwamna Ya Ƙara Gamuwa da Cikas, Kwamishina Ta 3 Ta Yi Murabus Daga Muƙaminta

Gwamna Ya Ƙara Gamuwa da Cikas, Kwamishina Ta 3 Ta Yi Murabus Daga Muƙaminta

  • Kwamishinar lafiya ta jihar Abia, Dr. Ngozi Okoronkwo ta miƙawa Gwamna Alex Otti takardar murabus daga muƙaminta
  • Okoronkwo ta yi murabus ne bayan dakatar da ita daga aiki bisa wasu zarge-zarge wanda aka kafa kwamiti domin gudanar da bincike
  • Gwamna Alex Otti ya amince da murabus din kwamishinar tare da yi mata fatan alheri da dukan ayyukan da za ta tasa a nan gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Kwamishinar lafiya a jihar Abia, Dr. Ngozi Okoronkwo ta yi murabus daga muƙaminta sama da wata ɗaya bayan dakatar da ita daga aiki.

Idan ba ku manta ba Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya dakatar da kwamishinar daga aiki domin gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da ake mata.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa, bayanai sun fito

Gwamna Alex Otti na jihar Abia.
Kwamishinar lafiya da aka dakatar ta yi murabus a jihar Abia Hoto: Alex Otti
Asali: Facebook

Sakataren yaɗa labaran gwamnan Abia, Njoku Ukoha ne ya bayyana murabus ɗin kwamishinar a wata sanarwa da ya fitar a Umuahia ranar Laraba, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ukoha ya ce Okoronkwo ta mika takardar murabus din ta ga Gwamna Otti a ranar Talata duk da kwamitin da aka kafa domin binciken ta bai kammala aikinsa ba.

Gwamna Otti ya amince da matakin Ngozi

Sanarwar ta ce tuni gwamnan ya amince da matakin da ta ɗauka kuma ya gode mata bisa yadda ta kawo sauyi a ɓangaren kiwon lafiya cikin shekara ɗaya.

Haka nan kuma Gwamna Otti ya mata fatan alheri da nasara a dukkan al'amuran da ta sa a gaba, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Alex Otti ya tuna amanar talakawa

Gwamnan ya kuma jaddada kudirinsa na kawo sauyi a jihar Abia, inda ya tunatar da al'umma nauyin amanar da suka ɗora masa na haɗa tawagar da za ta jagorance su.

Kara karanta wannan

Kotu ta amince 'danuwan Yahaya Bello da ake zargi da badakalar N3bn ya tafi kasar waje

"Gwamna Otti ya ƙara da cewa aikin da ke kansa ya haɗa da yiwa majalisar zartaswa ta jihar garambawul idan bukatar hakan ta taso domin cika alƙawurran da ya ɗauka," in ji Ukoha.

Dr. Ngozi Okoronkwo ta zama kwamishina ta uku da ta yi murabus daga gwamnatin Abia bayan kwamishinan kimiyya da fasaha da kwamishinan noma.

Tinubu ya karɓi Anyin zuwa APC

A wani rahoton kun ji cewa Gwamnan Imo kuma shugaban gwamnonin APC ya jagoranci Pius Anyim zuwa wurin Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa.

Hope Uzodinma ya gabatar da tsohon shugaban majalisar dattawan ga Tinubu bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262