Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Kamu, Daruruwan 'Yan Adawa Sun Dawo Cikinta a Kaduna
- Mambobin jam'iyyun adawa na PDP, APGA da LP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar
- Masu sauya sheƙar su 702 sun sauya sheƙar ne a mazaɓar Makera da ke ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu
- Shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar wanda ya tarbe su ya buƙace da su zaɓi ƴan takarar jam'iyyar a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Mambobi 702 na jam'iyyun LP, APGA da PDP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a jihar Kaduna.
Ƴan jam'iyyun adawan sun sauya sheƙar ne zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna a mazaɓar Makera ta ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu.
Sababbin shiga APC sun yi alwashi a Kaduna
Jaridar The Punch ta ce masu sauya sheƙar sun sha alwashin taimakawa jam'iyyar APC lashe zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe a ranar, 19 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanda suka sauya sheƙar zuwa APC sun haɗa da tsohon dan takarar majalisar dokokin jiha mai wakiltar mazabar Makera da shugabannin mata da matasa a ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu.
Sun samu tarba daga wajen shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar, Ibrahim Soso da tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna-Arewa, Sanata Lawal Aliyu a kasuwar 'Monday Market', da ke Kakuri Gwari, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Wace irin tarba suka samu a APC?
A nasa jawabin, Ibrahim Soso ya ba su tabbacin samun damarmaki a APC ba tare da la'akari da cewa yanzu suka shigo jam'iyyar ba.
Ya kuma buƙace su da su yi aiki tuƙuru tare da kaɗa ƙuri’a ga dukkanin ƴan takarar jam’iyyar APC a zaɓen kananan hukumomin da za a yi a ranar 19 ga watan Oktoba.
"Mun gamsu cewa Kaduna ta Kudu za ta zaɓi jam'iyyar mu ta APC kuma muna da yaƙinin cewa babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta mutu a nan."
- Ibrahim Soso
Mataimakin gwamna ya koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya watsar da jam'iyyar PDP mai mulki a jihar mai arziƙin man fetur.
Philip Shaibu wanda kotu ta dawo da shi kan muƙaminsa bayan tsige shi da majalisar dokokin jihar ta yi ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng