Bayan Hukuncin Kotu, Gwamnatin Kano Za ta Gudanar da Zaben Kananan Hukumomi

Bayan Hukuncin Kotu, Gwamnatin Kano Za ta Gudanar da Zaben Kananan Hukumomi

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta mutunta hukuncin kotun koli kan tabbatar wa kananan hukumomi 'yancin gashin kansu
  • Darakta Janar kan yada labaran gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya kara da cewa gwamnati ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi
  • Sanusi Bature ya kara da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba za ta tsoma baki a cikin harkokin gudanar da zabukan kananan hukumomi ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa shirye shirye sun yi nisa domin gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a Kano.

Kara karanta wannan

Bayani dalla dalla: Yadda za ku binciki kudin da kananan hukumominku ke samu duk wata

Gwamnatin ta ce shirya zaben wani bangare ne na bin umarnin kotun koli da ta tabbatar wa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano ta fara shirin zaben kananan hukumomi Hoto: Sanusi Bature
Asali: Facebook

Darakta janar kan yada labaran gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya wallafa haka a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf na mutunta doka da umarnin kotu, saboda haka za ta gudanar da zaben.

"Za a yi zabe mai inganci," Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar 44 cikin gaskiya da adalci.

Daily Trust ta wallafa cewa darakta janar kan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya fadi haka a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar NNPP da ya gudana a Kano.

Ya yi alkawarin cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba za ta yi katsalandan a cikin harkokin gudanar da zaben ba.

Kara karanta wannan

"Ban ce zan biya N80,000 ba," Gwamna ya musanta rahoton zai yi karin albashi

"Gwamnatinmu ta kyale shugabannin kananan hukumomi na baya sun kammala wa'adinsu duk da matsin lamba da mu ka rika samu."

- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Kano: An fara bijire wa Kwankwaso

A wani labarin mun ruwaito cewa rikicin cikin gida da jam'iyyar NNPP ke fuskanta ya fallatsa zuwa Kano inda Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fara shiga matsala.

Wasu daga 'ya'yan jam'iyyar sun fara bijire wa jagoran NNPP na kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Rabi'u Musa Kwankwaso a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.