Kaduna: Tsohon Kwamishina da Jiga Jigan PDP Sun Watsar da Ita, Sun Kama Layin Ganduje
- Kwana daya bayan sauya sheka da mataimakin gwamnan jihar Edo ya yi, wasu jiga-jigan PDP sun yi murabus daga jam'iyyar a Kaduna
- Tsohon sakataren gudanarwa na kasa a PDP da tsohon kwamishina a jihar Kaduna duk sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rigima tsakanin Gwamna Uba Sani da mai gidansa, Mallam Nasir El-Rufai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Tsohon sakataren gudanarwa na PDP a Najeriya, Mustapha Abubakar ya yi murabus daga jam'iyyar.
Mustapha jim kadan bayan murabus din na shi ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Kaduna.
Jiga-jigan PDP sun koma APC a Kaduna
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika da ya tura ga shugaban jam'iyyar a unguwar Gubuchi da ke karamar hukumar Makarfi, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon PDP ya bayyana cewa ya yi murabus din ne daga jam'iyyar saboda wasu dalilai na karan kansa, kamar yadda Tribune ta tattaro.
Tsohon shugaban ma'aikatan jihar ya yi godiya ga jam'iyyar da irin damarmaki da suka ba shi inda ya rike mukamai da dama.
Sauran wadanda suka koma APC a Kaduna
Sauran wadanda suka sauya shekan sun hada tsohon kwamishina, Rabiu Bako da tsohon sakataren din-din a jihar, Sulaiman Sambo.
Bako ya rike mukamin kwamishina a jihar Kaduna har sau biyar a lokacin mulkin PDP da aka yi a baya.
A ƴan kwanakin nan jiga-jigan jam'iyyar PDP da dama sun koma APC duk da kokawa da ake yi kan mulkinsu.
Mataimakin gwamnan Edo, Shaibu ya koma APC
A wani labarin mai kama da wannan, mun kawo muku cewa Mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu ya watsar da jam'iyyar PDP a jihar.
Shaibu wanda kotu ta dawo da shi kan mukaminsa bayan tsige shi ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jiya Asabar 20 ga watan Yulin 2024.
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a watan Satumbar 2024 da za mu shiga.
Asali: Legit.ng