2027: Ɗan Takarar Shugaban Kasa da Ya Sha Kaye Ya Gindaya Sharudan Tafiya da Atiku

2027: Ɗan Takarar Shugaban Kasa da Ya Sha Kaye Ya Gindaya Sharudan Tafiya da Atiku

  • Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya yi magana kan hadaka da jam'iyyun adawa domin kifar da gwamnatin Bola Tinubu
  • Peter Obi ya ce abin ya fi kamata yanzu shi ne kawar da yunwa da bakin talauci da ake fama da su ba maganar hadaka ba
  • Dan takaarar shugaban kasar a jam'iyyar LP ya ce idan har tafiya ce da za a kawo ci gaba to shi ma ya shirya amma sabanin haka ba ya ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi ya yi martani kan shirin hadaka domin kifar da gwamnatin APC.

Peter Obi ya ce ko kadan ba shi da shirin yin hadaka da jam'iyyun adawa musamman saboda zaben 2027 da ke tafe.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu: Sheikh Gumi ya karfafi guiwar matasa, ya soki malamai

Peter Obi ya gindaya sharudan amincewa da hadaka da Atiku
Peter Obi ya yi magana kan hadaka da Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi.
Asali: Twitter

Peter Obi ya gindaya sharuda ga Atiku

Tsohon gwamnan Anambra ya bayyana haka ne ga manema labarai a birnin Onitsha da ke jihar Anambra, kamar yadda Punch ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obi ya ce bai kamata a rika maganar hadaka ta siyasa ba bayan tulin matsalolin da Najeriya ke fama da su a halin yanzu.

Ya ce idan har aka yi kokarin kawo sauyi a kasar da kuma kawar da talauci da yunwa shi ne babban abin zai iya sanya shi a cikin hadakar.

Peter Obi ya bukaci kawar da talauci

"Ta yaya za a yi a cire mutane a kangin talauci? wannan shi ne babban abin da ya kamata ba wai hadakar jam'iyyu ba."
"Amma idan hadakar shi ne aiwatar da duka wadannan abubuwa da na fada to zan shiga nima a dama da ni amma sabanin haka ba na ciki."

Kara karanta wannan

Kano: Sarki Sanusi II ya koka kan halin kunci da ake ciki, ya yabawa gwamnatin Abba

"Ba zan taba yin tafiya kawai wanda 'yan siyasa za su ci gaba da satar kudin jama'a da hamdama da baba-kere ba wanda muke gani a yanzu."

- Peter Obi

2027: Watakila Buhari ya goyi bayan Atiku

Kun ji cewa yayin da ake tunkara zaben 2027, akwai hasashen cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya marawa Atiku Abubakar baya.

Akwai wasu dalilai manya-manya da dama da ake zaton watakila Buhari ya goyi bayan Atiku a zaben 2027 da ake tunkara a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.