Rikicin NNPP: An Bankado Halin da Kwankwaso Ke Ciki, an Fara Bijire Masa a Kano

Rikicin NNPP: An Bankado Halin da Kwankwaso Ke Ciki, an Fara Bijire Masa a Kano

  • Da alamu jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya shiga matsala kan rikicin cikin gida a jam'iyyar da ke faruwa
  • Shugaban jam'iyyar a yankin Arewa maso Yamma, Dakta Sani Danmasani ya ce an fara bijirewa sanatan musamman a Kano
  • Danmasani ya ce a yanzu Kwankwaso ba shi da wani wanda zai aminta da shi musamman daga cikin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP a Arewa maso Yamma ta bayyana matsalolin da Rabiu Kwankwaso ya shiga yayin da jam'iyyar ke fama da rikici.

Jam'iyyar ta ce Kwankwaso ya samu matsala da wasu masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi 44 na jihar yayin da suka fandare masa.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba bayan kazamin hari kan dan takarar gwamna a APC, an rasa rai

Shugaban NNPP ya fadi halin da Kwankwaso ke ciki a yanzu
Shugaban NNPP a Arewa maso Yamma ya fadi abin da ke faruwa da Rabiu Kwankwaso a jam'iyyar. Hoto: @KwankwasoRM.
Asali: Facebook

Rikicin NNPP ya jefa Kwankwaso a matsala

Shugaban jam'iyyar a yankin, Dakta Sani Danmasani shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Juma'a 19 ga watan Yulin 2024, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Danmasani ya ce akwai yiwuwar Kwankwaso zai janye jikinsa musamman a kan rigimar jam'iyyar da ke faruwa.

Ya ce akwai alamun Kwankwaso yanzu ya rasa wanda zai aminta da shi musamman masu ruwa da tsaki a jihar, Newstral ta tattaro.

"Kwankwaso yana cikin damuwa musamman yadda kwamandojin kananan hukumomi 44 a Kano ke bijire masa."
"Wannan matsala tana jefa shi a cikin damuwa wanda har iyalansa suka fara nuna damuwa kan halin da yake ciki."
"Ya tabbata a yanzu Kwanwkaso ya rasa wanda zai amince da shi ciki har da Gwamna Abba Kabir musamman kan rigima tsakaninsa da Gwamnatin Tarayya."

- Sani Danmasani

Kara karanta wannan

Wanda ya kafa NNPP ya ƙaryata bullar baraka a jam'iyya, ya fadi abin da ke faruwa

Danmasani ya ce Kwankwaso ya fadawa 'yan Kwankwasiyya cewa satifiket din jam'iyyyar na hannunsa wanda hakan ba gaskiya ba ne.

Ya ce uban jam'iyyar Dakta Boniface Aniebonam ya tabbatar da satifiket din na hannunsa kuma Kwankwaso bai taba ganin takardar ba.

Uban NNPP ya caccaki Kwankwaso kan jam'iyyar

Kun ji cewa wanda ya assasa jam'iyyar NNPP ya caccaki Sanata Rabiu Kwankwaso kan kawo rudani cikin jam'iyyar.

Dakta Boniface Aniebonam ya ce ya tsara komai domin kawo sauyi a kasar amma zuwan Kwankwaso ya dagula komai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.