Ondo: Dan Takarar Gwamna Ya Fadi Mafi Karancin Albashin da Zai Biya Idan Ya Ci Zabe
- Ayodele Olorunfemi, dan takarar gwamna na jam’iyyar LP a Ondo, ya ce zai biya N120,000 matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben gwamnan Obdo a ranar 16 ga watan Nuwamban 2024
- Mista Olorunfemi ya kuma lashi takobin gina tashar jiragen ruwa a jihar domin bunkasa tattalin arziki ma damar jama'a suka zabe shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Ayodele Olorunfemi, dan takarar gwamna na jam’iyyar LP a Ondo, ya ce zai amince da N120,000 a matsayin mafi karancin albashi idan ya ci zabe.
Mun ruwaito cewa a ranar 16 ga watan Nuwamba ne hukumar INEC ta shirya gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo.
Mista Olorunfemi ya ce akwai bukatar a biya mafi karancin albashi mai tsoka ga ma'aikata la'akari da yadda tsadar rayuwa ta ta'azza a kasar, inji rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan takara zai biya ma'aikata N120,000
Kafar yada labaran NAN ta ruwaito Mista Olorunfemi na cewa:
“Tun a shekarar 2023, lokacin da muke yakin neman zabe, mun tabbatar wa mutanenmu cewa LP za ta biya mafi karancin albashin N80,000 a Ondo.
“Amma la'akarin da halin da tattalin arzikin ke ciki yanzu, hadi da karin tsadar rayuwa, idan har aka zabe mu, ba za mu biya kasa da N120,000 a matsayin mafi karancin albashi ba.
"Wannan shi ne mafi ƙarancin albashin da zamu iya biya, kuma mun yi imanin za mu iya biya."
Dan takarar gwamnan LP zai bunkasa Ondo
Jaridar Vanguard ta rahoto dan takarar ya kuma yi alkawarin bunkasa kudaden shiga da ake samu a cikin jihar (IGR) ta hanyar daukar karin ma’aikata da inganta ayyukansu.
Idan aka zabe shi, Mista Olorunfemi ya ce gwamnatinsa za ta ba da fifiko wajen gina tashar jiragen ruwa ta tsandauri domin rage cunkoso yayin shiga Legas daga jihar.
“Idan jam'iyyar LP ta karbi mulki, abu na farko da za mu fara yi shine tabbatar da cewa akwai tashar jiragen ruwa a jihar Ondo domin bunkasa kasuwanci da tattalin arziki."
- A cewar dan takarar.
Ondo: APC ta bayyana dan takararta
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC da aka gudanar.
Aiyedatiwa, wanda ya gaji marigayi Rotimi Akeredolu a watan Disamba, ya yi nasara kan ƴan takara 15 a zaɓen fidda gwanin da aka gudanar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng