Jigon APC a Arewa Na Yi wa Tinubu Maƙarƙashiya? Gaskiya Ta Bayyana
- Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan ya bayyana gaskiya kan caccakar gwamnatin Bola Tinubu
- Ahmed Lawan ya yi bayani ne bayan an zarge shi da cewa mulkin Bola Tinubu ya kawo yunwa a fadin Najeriya kuma babu masu tanka masa
- Haka zalika Sanatan ya bayyana alakar da yake da ita da gwamnatin shugaba Bola Tinubu da yadda yake fata za ta cigaba da kasancewa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya yi martani bayan an zarge shi da sukan mulkin Bola Tinubu.
Sanatan mai wakiltar Yobe ta arewa ya bayyana yadda alakarsa ta ke da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Legit ta gano martanin da Ahmed Lawan ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da aka yiwa Ahmed Lawan
Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa wasu kafafen sadarwa sun wallafa cewa tsare-tsaren Tinubu sun kawo wahala a Najeriya.
Duk da wahalar da ake fama kuma an rasa samun wanda zai nuna masa gaskiya saboda shi dan kabilar Yoruba ne.
Ko Ahmed Lawan ya soki Tinubu?
Biyo bayan yada labarin a kafafen sadarwa, Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa sam bai fadi haka ba.
Sanatan ya ce yana goyon bayan Bola Tinubu har yau kuma ya yaba da ƙoƙarin da shugaban kasar yake wajen yaki da yunwa da wahalhalun rayuwa a Najeriya.
Ahmed Lawan: 'A guji yada jita jita'
Har ila yau, Sanata Ahmed Lawan ya yi kira ga al'ummar Najeriya su kaucewa yada labarai marasa tushe domin kaucewa barkewar rikici.
Ya kuma bayyana cewa waɗanda suka kirkiro labarin sun yi haka ne domin tayar da fitinar kabilanci a Najeriya.
2027: APC ta fara shirin zabe?
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da shugaban kasa Bola Tinubu ke cika shekara daya da yan watanni a kan karagar mulki, APC na shirin tsayar da shi takara.
An bayyana haka ne bayan hango allon hotunan Tinubu an kafe shi a babban birnin tarayya Abuja inda ake nuna bukatar sake zabarsa a shekarar 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng