Gwamna Ya Bayyana Dalilin Shiga Wahala a Najeriya, Ya Wanke APC Daga Zargi

Gwamna Ya Bayyana Dalilin Shiga Wahala a Najeriya, Ya Wanke APC Daga Zargi

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya wanke jam'iyyar APC daga zargin da ake kan cewa ita ta jawo wahalar rayuwa a Najeriya
  • Gwamna Hope Uzodimma ya bayyana haka ne yayin da gwamnonin APC suka kai ziyara ga shugaban jam'iyyar APC na kasa
  • Har ila yau, gwamnan ya bayyana abubuwan da za su ba jami'yyar APC nasara a zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban gwamnonin jami'yyar APC a Najeriya, Hope Uzodimma ya ce ba su suka jawo wahalar rayuwa a Najeriya ba.

Gwamna Hope Uzodimma ya bayyana cewa a zahiri jami'yyar APC ta kawo cigaba ne a tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Rashin aikin yi: Ganduje ya ba matasa shawarar abin da za su yi bayan kammala karatu

Gwamna Hope
Gwamna Hope ya ce APC ta yi kokari a Najeriya. Hoto: Hope Uzodimma.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamna Hope Uzodimma ya fadi haka ne yayin wata ziyara da suka kai ga Abdullahi Umar Ganduje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin wahalar rayuwa a Najeriya

A yayin ziyarar, gwamna Hope Uzodimma ya bayyana cewa tsadar rayuwa ba a Najeriya kawai ake fama da ita ba.

Hope Uzodimma ya kara da cewa matsin rayuwa matsalar ce ta tattalin arziki data shafi fadin duniya ciki har da Najeriya.

Uzodimma: 'APC ta yi kokari'

Gwamna Hope Uzodimma ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta yi matukar kokari wajen kawo cigaba a Najeriya.

Ya ce duk da matsalolin da shugaba Bola Tinubu ya samu amma yana kokarin samar da mafita wanda nan gaba kadan za a ga canji.

Zaben Edo: Abin da zai ba APC nasara

Gwamna Hope ya ce APC ce da mafi yawan gwamnoni a Najeriya kuma saboda haka za ta yi nasara a zabukan jihohin Edo da Ondo, rahoton Leadership

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya fara samun koma baya, shugabannin NNPP sun koma APC

Shugaban jami'yyar APC, Abdullahi Ganduje ya ce gwamnoni suna ba da gudunmawa sosai wajen cigaban jami'yyar kuma za su cigaba da aiki tare domin samun nasara.

Oshiomole ya yi alkawarin kawo APC a Edo

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole ya yi tsokaci kan zaben jihar Edo da ake shirin gudanarwa a watan Satumba.

Adams Oshiomole ya fadawa shugaba Bola Tinubu tabbacin APC za ta lashe zaben gwamna da za a yi kan jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng