Ana Shirin Zanga Zanga, Shugaban Malaman Izala Ya Fadi Wanda Za Su Zaba a 2027

Ana Shirin Zanga Zanga, Shugaban Malaman Izala Ya Fadi Wanda Za Su Zaba a 2027

  • A yayin da al'ummar Najeriya ke cigaba da kokawa kan mulkin Bola Tinubu malamin Izala ya bayyana dalilan zaben shi a 2023
  • Shugaban majalisar malaman kungiyar Izala, Dakta Ibrahim Jalo Jalingo ne ya bayyana dalilan zaben Tinubu da Kashim Shettima
  • Har ila yau, dakta Ibrahim Jalo Jalingo ya bayyana wanda za su zaba a babban zaben shugaban kasar 2027 idan Allah ya kai mu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Yayin da wasu al'ummar Najeriya ke kokawa kan zaben Musulmi da Musulmi a 2023, shugaban malaman Izala, Dakta Ibrahim Jalo Jalingo ya yi martani.

Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya bayyana dalilan da suka sanya yin kira a zabi Bola Ahmed Tinubu a zaɓen da ya gabata.

Kara karanta wannan

Bayan sun hana zanga zanga, malamai sun fara maganar ganin Tinubu domin samun mafita

Dakta Jalo Jalingo
Malamin addini ya fadi wanda za su zaba a 2027. Hoto: Ibrahim Jalo Jalingo
Asali: Facebook

Haka zalika malamin ya bayyana wanda za su zaba a 2027 a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin zaben Bola Tinubu a 2023

Dakta Ibrahim Jalo Jalingo ya bayyana cewa sun zabi shugaba Tinubu da Kashim Shettima ne saboda sun tsaya takara a tikitin Musulmi da Musulmi.

Dakta Jalo ya ce hakan ya tabbatar da cewa al'ummar Musulmi su ne mafi yawa a Najeriya kuma ba su nadama da ɗaukan matakin.

Sauran dalilan zaben Tinubu a 2023

Sheikh Jalo Jalingo ya bayyana cewa son komawar mulki kudu bayan dan Arewa (Muhammadu Buhari) ya kammala na cikin hikimar zaben Tinubu a 2023.

Malamin ya ce hakan zai kara hadin kan kasa da samar da tsaro maimakon a ce yan Arewa ne kawai ke mulki a Najeriya.

Dr. Jalo: 'Wanda za mu zaba a 2027'

Kara karanta wannan

Tinubu ya mayar da martani bayan harbin Donald Trump, ya yi gargadi

Har ila yau, babban malamin ya tabbatar da cewa har a shekarar 2027 za su kara zaben tikitin Musulmi da Musulmi idan suka tsaya takara.

Ya kuma bayyana cewa za su yi kira ga al'ummar Najeriya su zabi Musulmi da Musulmi saboda babu nadama a cikin hakan.

2027: CNEF ta kalubalanci Ali Ndume

A wani rahoton, kun ji cewa gamayyar ƙungiyar dattawan Arewa maso Gabas (CNEF) ta ja kunnen Sanata Ali Ndume kan sukar shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Ƙungiyar ta buƙaci sanatan da ya fito ya bayyana yadda ya gudanar da wakilcinsa a majalisa ko ya rasa kujerarsa a zaɓen 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng