Riga Malam Masallaci: An Hango Allon Kamfen Bola Tinubu na Zaben 2027

Riga Malam Masallaci: An Hango Allon Kamfen Bola Tinubu na Zaben 2027

  • Yayin da shugaban kasa Bola Tinubu ke cika shekara daya da yan watanni a kan karagar mulki, APC na shirin tsayar da shi takara
  • An hango allon kamfen Tinubu an kafe shi a babban birnin tarayya Abuja inda ake nuna bukatar sake zabarsa a shekarar 2027
  • An kafe allon ne a lokacin da 'yan Najeriya ke hankoron a samar da sauyin tsare-tsaren gwamnati don samun saukin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT, Abuja - 'Yan Najeriya na tsaka da bayyana rashin gamsuwa da yadda Bola Tinubu ke mulkar kasar, sai ga shi an fara shirye-shiryen ya sake tsayawa takara a 2027. An hango allon kamfen Bola Tinubu makale a babban birnin tarayya Abuja ko shekara biyu bai cika ba a mulkin kasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya mayar da martani bayan harbin Donald Trump, ya yi gargadi

Bola Ahmed Tinubu
An fara shirin tsayar da Tinubu zaben shugaban kasa a 2027 Hoto: Ajuri Ngelale/UGC
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa allon kamfen na dauke da Tinubu da mai dakinsa, Misis Remi a wani hoto irin na masoya.

2027: Ana shirin tsayar da Tinubu takara

Kungiyoyi irinsu Arewa Progressive Forum for Good Governance na cika-bakin Tinubu zai sake samun takara kuma za a zabe shi a kasar nan, Vanguard ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano wani allon kamfen Tinubu a Abuja wanda kungiyar Dark Matters ta dauki nauyin sanya wa a kusa filin wasa na kasa.

Wani bidiyo da Sahara Reporters ta wallafa ya nuna shugaban kasar rike da matarsa yayin da ake tallan sake zabarsa.

'Yan Najeriya na kuka da mulkin Tinubu

Al'ummar kasar nan na kokawa kan tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ta bijiro da su.

Akwai fargabar wasu dokoki da kudurorin gwamnatin na rage kaunar da ake yiwa shugaban kasar a yanzu.

Kara karanta wannan

"Hana makiyaya kiwo a sake zai jawo manyan matsaloli 3 a ƙasa," KACRAN

"Tinubu zai fadi zaben 2027," Jigon APC

A baya mun kawo labarin cewa wani jigo a jam'iyyar Bola Tinubu ta APC ya ce shugaban zai iya faduwa zaben 2027 mai zuwa.

Dan Bilki Kwamanda, wanda jigo ne a jam'iyyar APC reshen jihar Kano kuma masoyin tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya ce akwai kura-kurai da Tinubu ke tafkawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.