Adamawa: NNPP Ta Lashe Kujera 1 Yayin da Aka Sanar da Zaben Kananan Hukumomi
- Hukumar zabe a jihar Adamawa ta fitar da sakamakon zaben ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar
- Hukumar ta tabbatar da cewa jam'iyyar PDP mai mulki jihar ta lashe dukkan kujerun 21 na kananan hukumomi a jihar
- Shugaba hukumar a jihar, Mohammed Umar shi ya tabbatar da haka inda ya ce NNPP ta yi nasara a kujera daya ta kansila a jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa - Hukumar zabe a jihar Adamawa ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi a jihar.
Hukumar ta ce jami'yyar PDP ta lashe duka zaben da aka gudanar a ƙananan hukumomi a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024.
Adamawa: PDP ta lashe zaben ƙananan hukumomi
Shugaban hukumar a jihar, Mohammed Umar shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 14 ga watan Yulin 2024 a Yola, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umar ya ce jam'iyyar PDP mai mulki a jihar ita ta lashe duka kujerun kananan hukumomi 21 da mummunan kaye, Daily Post ta tattaro.
Ya ce PDP ta lashe duka unguwanni a jihar gida 226 inda jam'iyyar NNPP kuma ta ta yi nasara a kujerar kansila a unguwar Demsa a karamar hukumar Demsa da ke jihar.
Jihar Adamawa ita ta fara gudanar da zaben ƙananan hukumomi bayan hukuncin kotu game da ƴancinsu a makon da ya gabata.
Tattaunawar Legit Hausa da wani a Adamawa
Legit Hausa ta tattauna da wani ma'aikacin wuccin na hukumar INEC a jihar kan wannan zaɓe da aka gudanarwa.
Matashi wanda ya bukaci a boye sunansa saboda tsaro ya tabbatar da cewa NNPP ta samu nasara a zaben da aka gudanar a jihar.
Ya ce:
"Tabbas an samu kujerar kansila daya da jam'iyyar NNPP ta lashe a zaben da aka gudanar a jiya Asabar."
Fintiri ya maka Tinubu a kotun
A wani labarin, kun ji cewa an samu saɓani tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatin jihar Adamawa.
Lamarin ya kai gwamna Ahmadu Fintiri ya shigar da kara Babbar Kotun Tarayya da ke birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng