“Tinubu Zai Kife a 2027: Jigon APC a Kano Ya Gargadi Shugaban Kasa Kan Zabe
- Jigon jam'iyyar APC a Kano, Dan Bilki Kwamanda ya yi martani kan kura-kuran da gwamnatin Bola Tinubu ke aikatawa
- Dan Bilki ya ce yadda APC ke gudanar da mulki idan har bata gyara ba za ta samu gagarumar matsala a zaben 2027 da ke tafe
- Ya ce sun jinginar da CPC domin su dawo a kafa jam'iyyar APC amma har yanzu yaudararsu ake yi ba tare da taimakonsu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jigon jam'iyyar APC a jihar Kano, Dan Bilki Kwamanda ya yi magana kan mulkin Bola Tinubu a Najeriya.
Kwamanda ya ce akwai matsala ga jam'iyyar APC idan har ba ta yi gyara kan yadda take gudanar da mulki ba.
2027: Jigon APC ya gargadi Tinubu
Jigon APC ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo yayin wata hira da @jrnaib2 ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan Bilki ya ce an yaudare su a gwamnatin APC inda ya ce ko kusa idan ba ta yi gyara ba za ta rasa zaben 2027.
Ya ce idan zabe ya zo za su gane kuskurensu idan har Tinubu bai gyara matsalolin da ake fuskanta ba a yanzu.
Dan Bilki ya bukaci Tinubu ya gyara
"Wallahi idan har APC ba ta gyara kura-kurenta a zaben 2027 wallahi ba za ta ci zabe ba."
"Ba wai Tinubu ya san hanyoyin cin zabe ba ko mene ya sani mutane suna da hankali suna da basira ba za su yadda da APC ba."
"Mu da muka da muka jinginar da CPC aka gina APC da mu sun yi watsi damu kuma ba su taimakonmu sai dai yaudara da karya."
- Dan Bilki Kwamanda
Dan Bilki ya ce kalilan ne suke taimakonsu a cikin jam'iyyar inda ya ce kwata-kwata an mayar da su saniyar ware.
APC ta caccaki NNPP a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta soki martanin NNPP na cewa Bola Tinubu zai samu matsala a zaben 2027 da ke tafe.
Shugaban jam'iyyar a Kano, Abdullahi Abbas shi ya bayyana haka inda ya ce NNPP ce za ta samu matsala ganin yadda take mulkin jihar.
Asali: Legit.ng