An Bukaci a Dakatar da Ministan Tinubu daga PDP, An Kawo Dalilai
- Jam'iyyar PDP na zargin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da hannu a rikicin da ya dabaibaye ta a jihar Edo
- Wasu mambobin jam'iyyar sun buƙaci a dakatar da tsohon gwamnan na jihar Rivers saboda kitsa wutar rikicin da jam'iyyar ke fama da shi a Edo
- Tun bayan kammala zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar Edo, PDP ta tsinci kanta cikin rikicin cikin gida
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Jam’iyyar PDP ta zargi tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da hannu a rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar reshen jihar Edo.
Jam’iyyar PDP a jihar Edo ta fuskanci rigingimun cikin gida tun bayan zaɓen fidda gwani na gwamna a ranar 22 ga watan Fabrairun 2024, wanda ya Asue Ighodalo lashe.
Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na ƙasa, Timothy Osadolor, a wata hira da ya yi da jaridar The Punch, ya tabbatar da cewa shugabancin jam’iyyar zai ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da nasarar ɗan takarar jam’iyyar PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me yasa ake so PDP ta dakatar da Wike?
Wani mamba a kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar (NWC) da ya nemi a sakaya sunansa, saboda ba shi da izinin yin magana a kan lamarin ya zargi Wike da hannu a rikicin jam’iyyar a jihar Edo.
"Mun damu matuƙa, kuma shugabannin jam’iyyar na da irin wannan damuwar, yadda wasu ƴaƴan jam’iyyar ke yunƙurin yi wa ƙoƙarin jam’iyyar zagon ƙasa a jihar Edo."
"Dan Orbih da tsohon mataimakin gwamna, Philip Shaibu, ba su kaɗai suke aiki ba. Suna aiki tare da Nyesom Wike. Ministan yana yin duk mai yiwuwa domin yiwa gwamnan Edo, Godwin Obaseki zagon ƙasa, ta yadda APC za ta yi nasara."
"Kamar yadda lamarin yake a jihar Rivers, shugabannin jam’iyyar PDP na sane da cewa Wike ne ke bayar da kuɗaɗe da kuma rura wutar rikicin da ke cikin jam’iyyar a jihar Edo."
"Lokaci ya yi da ya kamata jam’iyyar ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan wannan lamarin tare da dakatar da Wike."
- Wani mamban NWC
Jigon PDP ya fice daga jam'iyyar
A wani labarin kuma, kun ji cewa Daniel Bwala, lauya kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa a ƙasar nan ya bayyana cewa ya jima da barin babbar jam'iyyar adawa PDP.
Daniel Bwala ya ce bayan barin PDP, a yanzu yana dab da sauya sheƙa zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin Najeriya.
Asali: Legit.ng