Rashin Katabus: An Bayyana Lokacin da Tinubu Zai Yi Garambawul a Muƙaman Ministoci
- Daniel Bwala ya yi martani ga Sanata Ali Ndume kan caccakar gwamnatin Bola Tinubu da yake yawan yi
- Bwala ya ce Ndume bai kai ya soki gwamnatin Tinubu ba inda ya kalubalance shi ya nuna ayyukan daya yi a mazabarsa
- Lauyan ya ce nan da kwanaki ko makwanni Tinubu zai yi garambawul a Ministocinsa bayan tattara bayanai kan kokarinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon na hannun daman Atiku Abubakar ya yi martani kan Ministocin Shugaba Bola Tinubu.
Danielle Bwala ya ce nan da ƴan kwanaki kadan Tinubu zai yi garambawul a mukaman Ministocinsa domin gyara al'amura.
Tinubu: Bwala ya yi martani ga Ndume
Bwala ya bayyana haka ne yayin da yake martani ga Sanata Ali Ndume kan caccakar Tinubu da ya yi, Daily Trust ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan ya ce Ndume bai kai ya soki gwamnatin Tinubu ba inda ya kalubalance shi ya nuna ayyukan da ya yiwa mazabarsa.
Har ila yau, Bwala ya ba da tabbacin cewa Tinubu zai yi garambawul bayan tattara bayanan kokarin da kowane Minista ya yi.
Bwala ya ce an kusa yin garambawul
"Ali Ndume yana yawan caccakar Bola Tinubu da mukarrabansa, ya manta irinsu ne da gwamnoni da ƴan jam'iyya suka kawo Ministocin."
"Shugaba Tinubu ya sha fada cewa ba zai gudanar da gwamnatin da ba za a yi garambawul ba kamar yadda Buhari ya yi "
"Kwanan nan aka kammala duba ayyukan kowane Minista, kuma nan da kwanaki ko makwanni Tinubu zai yi garambawul."
- Daniel Bwala
Ndume ya caccaki tsarin mulkin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya dira kan Shugaba Bola Tinubu inda ya caccaki yadda ya ke tafiyar da mulkinsa a Najeriya.
Ndume ya ce Tinubu ya kebe kansa bai san abin da ke faruwa ba a kasa inda ya ce mafi yawansu ba su iya ganinsa a lokacin da suke so.
Daga bisani Ndume ya gargadi gwamnatin da ta yi mai yiwuwa domin kawo karshen halin da al'umma suke ciki a yanzu.
Asali: Legit.ng