Majalisa Ta Ci Gaba da Zama, Kudirin Kirkirar Sabuwar Jiha Ya Tsallake Karatu Na 2
- Yayin da ake ta kokarin kirkirar sababbin jihohi a Najeriya, a yau kudirin samar da jihar Etiti ya tsallake karatu na biyu
- Majalisar ta ci gaba da zamanta ne a yau Alhamis bayan katse zaman a jiya saboda mutuwar mambanta daga jihar Oyo
- Wannan na zuwa ne bayan gabatar da kudirin kirkirar sabuwar jihar 'Tiga' daga Kano wanda Kawo Sumaila ya gabatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Majalisar Wakilan Najeriya ta ci gaba da zama a yau Alhamis bayan mutuwar mambanta a jiya Laraba 10 ga watan Yulin 2024.
Majalisar yayin zamanta ta an gabatar da kudurorin kirkirar sababbin jihohi inda kudirin jihar Etiti ya tsallake karatu na biyu.
Majalisa ta duba kudirin sabuwar jihar Etiti
Kudirin na neman kirkirar sabuwar jihar ce da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya da ke da jihohi biyar kacal, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabuwar jihar idan ta kankama za ta kunshi kananan hukumomi 11 da za a cire daga yankin gaba daya, The Nation ta tattaro.
Hon. Amobi Godwin Ogah ya bayyana cewa samar da jihar zai tabbatar da yankin kamar sauran yankuna da ke da jihohi fiye da biyar.
Etiti: Mambobin da suka ba da gudunmawa
Sauran mambobin da suka yi hadin guiwa wurin gabatar da kudirin akwai Hon. Miriam Onuoha da Hon. Kama Nkemkama.
Sai kuma mambobin Majalisar kamar Hon. Princess C. Nnabuife da kuma Hon. Anayo Onwuegbu.
Ogah ya ce yayin da sauran yankuna ke da jihohi shida da kuma Arewa maso Yamma mai jihohi bakwai, Kudu maso Gabas ne kadai ke da biyar.
Bayan wanna akwai kudurori da ke neman kirkirar sababbin jihohi a Najeriya cikin har da jihar Tiga daga Kano da Lagos da sauran jihohi.
Sumaila ya gabatar da kudirin sabuwar jiha
A wani labarin, kun ji cewa Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya gabatar da kuduri a Majalisar Dattawa a Najeriya.
Sumaila ya gabatar da kudirin ne domin neman kirkirar sabuwar jihar 'Tiga' daga Kano a jiya Laraba 10 ga watan Yulin 2024.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rigimar sarauta a jihar bayan Abdullahi Ganduje ya daddatsa masarautu.
Asali: Legit.ng