Kwankwaso Ya Barar, Dan Takarar Gwamna Ya Yi Murabus a Gombe, Ya Tura Sako
- Jagoran jam'iyyar NNPP kuma dan takarar gwamnan jihar Gombe, Hon. Khamisu Mailantarki ya yi murabus
- Mailantarki ya sanar da yin murabus din ne a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024 a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu
- Legit Hausa ta ji ta bakin sakataren jam'iyyar a Gombe, Muhammad Baba Sherrif kan wannan murabus na Mailantarki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Gombe - Jam'iyyar NNPP ta tafka babban rashi bayan dan takarar gwamnanta daga jihar Gombe ya yi murabus.
Jagoran jam'yyar a Gombe kuma dan takarar gwamna, Hon. Khamisu Mailantarki ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar.
Jigon NNPP ya yi murabus daga jam'iyyar
Jigon jam'iyyar kuma tsohon dan takarar shugabancin karamar hukumar Gombe, Adamu Babale Makera shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Murabus din Mailantarki na kunshe ne a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024.
A cikin wasikar, Mailantarki ya yi godiya ga shugabannin jam'iyyar game da damar da suka ba shi wurin gina siyasarsa.
Har ila yau, ya kuma mika godiya ga sauran mambobin jam'iyyar da suka nuna masa goyon baya musamman a takarar zaben 2023.
Mailantarki ya yi godiya ga jam'iyyar NNPP
"Ina mai sanar da ku cewa na yi murabus a matsayin mamban jam'iyyar NNPP daga yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024."
"Kasancewa da ku da sauran mambobin jam'iyyar abin alfahari ne wanda ya yi matukar tasiri a siyasa ta, ina godiya da damar da kuka ba ni."
"Ina matukar godiya ga shugabanni da mambobin jam'iyya da goyon baya da suka nuna min a takarar 2023 na neman gwamnan jihar Gombe."
- Khamisu Mailantarki
Legit Hausa ta tattauna da sakataren jam'iyyar
Legit Hausa ta ji ta bakin sakataren jam'iyyar a Gombe, Muhammad Baba Sherrif kan wannan murabus din Mailantarki
Ya ce tabbas sun yi rashin jigo inda ya ce babu jam'iyyar da ba za ta so ya kasance tare da ita ba.
"Rashin jigo irin Hon. Mailantarki rashi ne da duk wanda ya san siyasa ba zai ji dadi ba, daga lokacin da na iske takardan murabus dinsa, wallahi kai kace mutuwa aka min."
"Domin Mailantarki cikakken dan siyasa ne da babu jam'iyyar da ba za ta so kasancewarsa cikinta ba."
"Amma ya zama wajibi mu mutunta ra'ayinsa tare da yi masa fatan alkairi a duk inda zai samu kansa, muna addu'ar Allah ya sa ficewar ta zama alkairi."
- Muhammad Baba Sherrif
Edo: NNPP ta karbi sabbin tuba 2,000
A wani labarin, kun ji cewa Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo, jami'yyar NNPP ta karbi sabbin tuba daga wasu jam'iyyu.
Dan takarar gwamnan jihar, Fasto Azehme Azena shi ya karbi sabbin tuban yayin tattakin zaman lafiya a ranar Alhamis 27 ga watan Yunin 2024.
Asali: Legit.ng