Rikicin Sarautar Kano: APC Ta Fadi Abin da Zai Faru da Tinubu a Kano a Zaɓen 2027
- Shugaban jam'iyyar APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya ce Abba Gida-Gida na amfani da rikicin sarauta wajen rufe gazawarsa
- Alhaji Abbas ya ce wannan rikicin sarautar da jihar ke fuskanta kadai ya isa yasa masu kada kuri'a su kayar da NNPP a zaben 2027
- Shugaban jam'iyyar adawa a Kano, ya ce Tinubu zai samu kuri'a ninki uku na abin da ya samu a zaben 2023 idan zaben 2027 ya zo
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya yi martani ga Hashimu Dungurawa, shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano kan maganganunsa.
An ruwaito cewa Hashimu Dungurawa ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sha mugun kaye a jihar Kano idan zaben shekarar 2027 ya zo.
Shugaban jam'iyya mai mulki ta NNPP a jihar Kano, ya ce wannan zai faru ne sakamakon rikicin sarautar da ya ki ci balle cinyewa a jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Tinubu zai samu kuri'u a Kano" - APC
To sai dai a wata takardar martani da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, Alhaji Abbas ya ce yanzu APC ta fi samun hadin kai wanda zai sa Tinubu ya samu mafi rinjayen kuri'u a 2027.
Ya jaddada cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoran NNPP, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso za su sha kaye saboda rashin iya mulki.
A cewar takardar martanin:
"Rikicin da ya dabaibaye tsagin jam'iyyar NNPP da jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna tsantsar gazawar jam'iyyar."
APC: "Gwamnatin NNPP ta gaza a Kano"
Jaridar Vanguard ta ruwaito shugaban APC na Kano ya cigaba da cewa, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta NNPP a Kano ta gaza yin abin kirki a shekara daya na mulkinta.
"A yayin da sauran gwamnonin jihohi ke kaddamar da ayyuka, ita gwamnatin Kano ta na amfani da rikicin sarauta wajen janye hankalin jama'a ga gazawarta."
- Inji Alhaji Abbas.
Kwankwaso zai ci zabe a 2027?
Shugaban jam'iyyar na APC ya ce Rabiu Kwankwaso ba shi da kwarewa da gogewar da zai sa ya ci zaben shugabancin kasa a babban zaben 2027.
A zaben da ya gabata, Kwankwaso ya zo na hudu ne duk da ya yi nasara a jihar Kano.
Farfesa ya shawarci Aminu da Sanusi II
A wani labari na daban, Farfesa Umar Labdo ya sbada muhimmiyar shawara ga Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido II da tsohon Sarkin Kano, Aminu Bayero.
Farfesa Labdo ya ce da tun farko sun yi koyi da kakan Sanusi Lamido da abin bai kai su ga hakan ba domin wannan rikicin nasu na cikin gida ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng