Tsohon Jigon APC Ya Ba Atiku, Peter Obi Lakanin Kayar da Tinubu a Zaben 2027
- Salihu Lukman ya shawarci jagororin ƴan adawa a Najeriya da su yi haɗaka domin kawo ƙarshen mulkin jam'iyyar APC a zaɓen 2027
- Tsohon jigon na jam'iyyar APC ya nuna cewa dole sai ƴan adawan sun yi haɗaka domin raba Shugaba Tinubu daga madafun ikon ƙasar nan
- Daga cikin waɗanda Salihu ya buƙaci su zo a yi haɗakar da su akwai Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso, Nasir El-Rufai da sauransu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon jigo a jam'iyyar APC, Salihu Lukman ya yi kira ga manyan ƴan siyasa a Najeriya da su dunƙule waje ɗaya domin kawar da APC daga kan madafun iko.
Salihu Lukman wanda ya yi murabus daga APC ya yi kira ga Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso da Rotimi Amaechi da su haɗa kai domin kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
A cikin waɗanda Salihu Lukman ya buƙaci su zo a yi haɗakar da su akwai irin su tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, Nasir El-Rufai, Rauf Aregbesola, Kayode Fayemi, Ibikunle Amosun da sauran manyan ƴan siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon jigon APC ya ba ƴan adawa shawara
Tsohon jigon na jam'iyyar APC ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja, ranar Lahadi, cewar rahoton tashar Channels tv.
A cikin sanarwar mai taken 'Makomar dimokuraɗiyyar Najeriya', Salihu Lukman ya ce gina irin haɗin kan da zai iya ciyar da dimokuradiyyar Najeriya gaba yana bukatar rashin son kai daga ɓangaren shugabannin siyasar Najeriya.
"Dole ne jagororin adawa a Najeriya da jagororin APC da aka hana shiga gwamnatin Tinubu irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, Kayode Fayemi, Ibikunle Amosun, Nasir El-Rufai, Rauf Aregbesola da sauransu su haɗa kai domin ceto Najeriya."
"Ko samar da haɗakar zai iya yiwuwa ta hanyar jam'iyyun da ake da su, kafa sabuwar jam'iyya ko yiwa wata jam'iyyar kwaskwarima, mataki ne wanda za a iya cimmawa idan shugabannin suka yarda su haɗa kansu."
- Salihu Lukman
Salihu Lukman ya caccaki manufofin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Salihu Lukman ya yi magana kan tsare-tsaren Bola Tinubu.
Salihi Lukman ya ce matakan da Tinubu ke dauka sun fi yiwa yankinsa na Kudu maso Yammacin ƙasar nan illa fiye da kowane yanki.
Asali: Legit.ng