Samoa: Gwamnati Ta Magantu Kan Ikirarin ’Yan Arewa Za Su Guji Tinubu a 2027

Samoa: Gwamnati Ta Magantu Kan Ikirarin ’Yan Arewa Za Su Guji Tinubu a 2027

  • Bayan sanya hannu a yarjejeniyar Samoa, 'yan Arewa da dama sun dawo daga rakiyar Shugaba Bola Tinubu a yanzu
  • Wasu suna danganta hakan ne da yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu da ake zargin akwai auren jinsi
  • Sai dai hadimin shugaban, Dada Olusegun ya ce abin ake fada duk magana ne, 'yan Arewa na tare da Tinubu kamar yadda suka yi a baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Malaman Musulunci da dama a Arewa sun caccaki Bola Tinubu kan yarjejeniyar Samoa da aka sanyawa hannu.

Hakan ya biyo bayan sanya hannu a yarjrjniyar da wasu ke zargin akwai auren jinsi a ciki da ya saba addinin Musulunci da Kiristanci.

Kara karanta wannan

Samoa: Tinubu zai dauki mataki kan Daily Trust game da rahoton yarjejeniyar da aka yi

Ana hasashen 'yan Arewa za su watsewa Tinubu a zaben 2027 kan Samoa
Gwamnati ta yi martani kan ikrarin Arewa za ta guji Tinubu a zaben 2027 saboda yarjejeniyar Samoa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Gwamnati ta ce Arewa na tare da Tinubu

Hadimin Bola Tinubu a bangaren yada labarai, Dada Olusegun ya yi tsokaci kan lamarin inda ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun ya ce ba kamar yadda ake yadawa ba 'yan Arewa ba su da matsala da Tinubu a zaben 2027 da ke tafe.

Ya ce bai kamata wasu masu mugun nufi suna ikararin cewa 'yan Arewa za su juya baya ga Tinubu ba lokacin zabe.

Har ila yau, Olusegun ya ce har yanzu Bola Tinubu yana da goyon baya a Arewa kuma shi za su sake zaba a 2027 kamar yadda suka yi a 2023.

Gwamnati ta bugi kirji kan zaben 2027

"Don Allah mu bar yada abin da bamu da masaniya a kai musamman wurin yin jam'i a maganganunmu."

Kara karanta wannan

A karo na 7, Sayyada Sadiya Haruna, tsohuwar matar G Fresh zata amarce

"Yan Arewa ba su da matsala da Bola Tinubu, wasu masu mugun nufi ne da ke goyon bayan Alhaji Koojoli da muka kayar a 2023."
"Mafi yawan 'yan Arewa sun zabi Tinubu a zaben 2023 a kansa, kuma haka za su sake yi a zaben 2027 mai zuwa."

- Dada Olusegun

Tinubu zai maka Daily Trust a kotu

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya za ta dauki mataki kan rahoton Samoa da ake yadawa wanda ya sha bam-ban da abin da ta sanyawa hannu.

Gwamnatin Bola Tinubu ta ce za ta dauki matakin shari'a musamman kan Daily Trust saboda yawan kawo rahotanni marasa inganci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.