Tsohon Kwamishina Ya Fallasa Gwamnati, An Gano Uba Sani Yana ‘Karya’ da Ayyukan El Rufai
- Jafaru Sani ya fito ya kare Nasir El-Rufai wanda ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna suka taso shi a gaba
- Tsohon kwamishinan ya musanya zargin da ake yi a kan batun bashi, ya yi bayanin irin ayyukan da aka yi
- ‘Dan siyasar ya zargi Uba Sani da fakewa da ayyukan da aka yi tun a gwamnatin El-Rufai, yana nuna nasu ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Jafaru Sani ya dauki lokaci ya kare gwamnatin Nasir El-Rufai daga zargin cewa ta yi awon gaba da dukiyar al’ummar Kaduna.
Akwai zargin da majalisar dokoki ta ke yi na cewa an karkatar da N423bn a lokacin da Nasir El-Rufai ya yi mulki daga 2015 zuwa 2023.
Kwamishinan Nasir El-Rufai ya kare shi
A wani fai fai da wani Imran U Wakili Oluwa Femi ya wallafa a shafin X, Jafaru Sani ya musanya wadannan zargi, har ya yi martani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton kwamitin binciken majalisar Kaduna ba komai ba ne face karya da soki-burutsu a wajen Jafaru Sani wanda ya yi kwamishina.
El-Rufai da zargin 'yan majalisar Kaduna
Amma a wata hira da aka yi wani ‘dan majalisar dokokin Kaduna a tashar Channels, ya bayyana akasin ikirarin Malam Ja’afar Sani.
Honarabul Henry Marah ya ce majalisa ba ta amince da wasu daga cikin bashin da gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta karbo ba.
Tsohon kwamishinan ya ce suna nan a kan bayanin da El-Rufai ya yi game da basussukan jihar a lokacin da yake mika mulki.
Uba Sani yana dauraye ayyukan El-Rufai?
Har ila yau, Jafaru Sani ya caccaki gwamnatin Uba Sani da ya zarga da ikirarin ita ta yi wasu ayyuka da a zamanin El-Rufai aka yi su.
An yi misalai da katafaren dakin bincike, makarantun kimiyya da wasu 62 a karkashin tsarin Agile da kayan asibitocin shan magani 250.
Sannan ya yi karin haske cewa cikin ayyukan da Uba Sani yake tunkaho da su akwai wadanda tun kafin El-Rufai aka samo kudinsu.
Malam Jafaru Sani yana maida martani ne ganin gwamnatin Kaduna ta na kukan an ci bashi kuma ba a san ina kudin suka shige ba.
Gwamna Uba ya koka da bashin El-Rufai
Kwanaki aka samu labari Gwamna Uba Sani ya fadi bashin da aka ci a Kaduna da kudin da Nasir El-Rufai ya bari a asusun jihar Kaduna.
Uba Sani ya ce kason jihar na tafiya ne a biyan bashin da aka ci. Sai dai shi ya dafe aka karbo bashin a lokacin yana majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng