Dambarwar Sultan: Dalilai da Ka Iya Jawo Gwamna Aliyu Rasa Kujerarsa a 2027
- Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya tube sarakuna akalla 15 bayan hawansa karagar mulkin jihar.
- Gwamnan na wa'adinsa na farko yayin da yake daukar matakai da ake ganin ka iya jawo masa matsala a 2027
- Ahmed Aliyu ya kirkiri wata doka da za ta rage karfin ikon Sarkin Musulmi wurin nadin hakimai a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Gwamna Ahmed Aliyu na daga cikin gwamnonin da ke wa'adinsu na farko kan kujerar mulki.
Wasu na ganin gwamnan ka iya rashin nasara a zaben 2027 saboda wasu matakai da ya ke dauka a jihar.
Sokoto: Aliyu ya tube sarakuna 15
Gwamnan ya tube sarakuna 15 saboda aikata wasu laifuffuka daban-daban wanda ake ganin za su iya jawo masa matsala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmed ya kuma kirkiri wata sabuwar doka wacce za ta rage karfin ikon Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar a jihar.
Idan aka sanya hannu a dokar, Sultan zai rasa ikonsa na nadin hakimai a jihar kai tsaye kamar yadda ya saba.
A sabuwar dokar, dole sai da sahalewar gwamna kafin Majalisar Sarkin Musulmi ta nada hakimi sabanin abin da yake a baya.
Shettima ya gargadi gwamnatin Sokoto
Yayin da ake ganin dokar bata saba ka'ida ba tun da an bi tsarin Majalisa, wasu na ganin hakan barazana ne ga zabensa a 2027.
Yayin da ake cikin rigimar, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi gargadi ga gwamnan kan illar taba sarkin Musulmi.
Wannan gargadi na Shettima ba iya rikicin addini zai kare ba har ma da nuna ba su tare da matakin saboda zaben Tinubu a 2027.
An gargadi gwamnan Sokoto kan Sultan
A wani labarin, kun ji cewa cibiyar dabbaka shari'ar Musulunci ta gargadi gwamnatin Sokoto kan taba kimar Sarkin Musulmi.
Cibiyar ta yi gargadin ne yayin da ake kokarin kirkirar sabuwar doka da zata rage karfin ikon Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar a jihar
Asali: Legit.ng