Kotu Ta Dauki Mataki Kan Shari'ar Neman Tumbuke Ododo Daga Kujerar Gwamna

Kotu Ta Dauki Mataki Kan Shari'ar Neman Tumbuke Ododo Daga Kujerar Gwamna

  • Yayin da ake ci gaba da shari'a kan zaben gwamnan jihar Kogi, Kotun Daukaka Kara ta yi zama kan dambarwar
  • Kotun ta tanadi hukunci kan shari'ar da Murtala Ajaka na SDP ke kalubalantar zaben da aka gudanar a watan Nuwambar 2023
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani mazaunin garin Okene a jihar Kogi kan wannan hukunci na Kotun Daukaka Kara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta dauki mataki kan shari'ar zaben jihar Kogi.

Kotun ta tanadi hukunci a shari'ar da ɗan takarar SDP, Murtala Ajaka ke kalubalantar zaben wanda Usman Ododo ya yi nasara.

Kara karanta wannan

An jikawa PDP aiki, kotu ta yi hukunci kan zaben fidda gwani ana daf da zabe

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamna Kogi
Kotun Daukaka Kara ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kogi. Hoto: Usman Ododo, Murtala Ajaka.
Asali: Twitter

Ododo: Matakin da kotun ta ɗauka

Alkalan kotun guda uku sun tanadi hukunci tare da tabbatar da tuntubar bangarorin biyu kan ranar sake zama kan dambarwar zaben, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan masu kara, Pius Akubo ya bukaci kotun ta rusa hukuncin karamar kotu tare da tabbatar da Ajaka wanda ya lashe zaben.

Akubi ya ce hukuncin karamar kotun da ta tabbatar da nasarar Usman Ododo ya saba ka'idojin shari'a, Punch ta tattaro.

Lauyan Ododo ya roki kotu alfarma

A martaninsa, Cif Kanu Agabi da ke bangaren hukumar INEC ya bukaci kotun ta yi watsi da bukatar Ajaka kan soke zaben da aka gudanar a jihar.

Har ila yau, lauyan Ododo, Joseph Daudu ya ce babu gamsassun hujjoji kan korafin da SDP ta shigar.

Daudu ya kuma bukaci kotun ta yi watsi da korafi kan takardun bogi da ake yi kan Ododo inda ya ce matsala ce kafin zaɓe.

Kara karanta wannan

Borno: Majalisar dattawa ta faɗi sakacin da ya jawo aka kai harin bam a Gwoza

Legit Hausa ta ji ta bakin wani mazaunin garin Okene a jihar Kogi kan wannan hukunci na Kotun Daukaka Kara.

Abubakar Sadik Ja'afar ya ce babu makawa Usman Ododo ne ya lashe zaben da aka gudanar da rata mai yawa.

Sadik ya ce ya kamata Murtala Ajaka ya hakura da shari'ar ya ba Ododo dama ya ci gaba da ayyukan raya kasa.

Kotu ta yi hukunci kan rigimar sarauta

A wani labarin, kun ji cewa Kotun Koli ta yi hukunci kan rigimar sarauta da aka daɗe ana yi a jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya.

Kotun ta yi fatali sa korafin Michael Onakoya da aka tube a matsayin Sarkin Igbooye da ke Ipe a jihar shekaru da suka wuce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.