Sarautar Kano: NNPP Ta Yi Hannun Riga da Kwankwaso Kan Zargin Tasa Tinubu a Gaba

Sarautar Kano: NNPP Ta Yi Hannun Riga da Kwankwaso Kan Zargin Tasa Tinubu a Gaba

  • Jam'iyyar NNPP a Najeriya ta yi tsokaci kan zargin Rabiu Kwankwaso da rubuta wata takarda ga ƴan Majalisunta kan rigimar sarauta
  • Jam'iyyar ta barranta kanta da wasikar inda ta ce ba ta da masaniya wurin rubuta wasikar kuma ba da yawunta aka dauki matakin ba
  • Hakan ya biyo bayan zargin rubuta wasika ga ƴan Majalisun NNPP domin tasa Bola Tinubu a gaba saboda hannu a rigimar sarautar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP a Najeriya ta barranta kanta da zargin rubuta wasika da Rabiu Kwankwaso ya yi ga ƴan Majalisunta na Tarayya.

Jam'iyyar ta ce Sanata Rabiu Kwankwaso ya rubuta wasika ga 'yan majalisa domin sukar Bola Tinubu kan dambarwar sarautar Kano.

Kara karanta wannan

Rigimar sarauta: Farfesa a Kano ya zargi Kwankwaso da saka siyasa tun farkon lamarin

NNPP ta yi magana kan wasikar da Kwankwaso ya tura ga ƴan Majalisa
Jami'yyar NNPP ta yi fatali da wasikar da Kwankwaso ya rubutawa ƴan Majalisa kan rigimar sarauta. Hoto: Rabiu Kwankwaso, Agbo Gilbert.
Asali: UGC

NNPP tayi martani kan 'wasikar' Kwankwaso

NNPP a cikin wata sanarwa ga Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ta ce ba da yawunta Kwankwaso ya yi hakan ba, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata kungiya ce ta bankado cewa Sanata Kwankwaso ya rubuta takarda inda yake umartar mambobin Majalisar na NNPP su tasa Tinubu a gaba kan zargin hannu a rigimar sarauta.

Shugaba jam'iyyar, Agbo Gilbert da sakatarensa, Kwamred Oginni Olaposi Sunday sun bukaci Majalisar ta yi watsi da umarnin Kwankwaso, Leadership ta tattaro.

Kano: NNPP ta barranta kanta da Kwankwaso

"Mun samu labarin wata takarda da ke yawo da saka hannun Dakta Ajuji Ahmed da aka rubuta ga Majalisar Tarayya."
"Muna son tabbatar da cewa wasikar da Dakta Ajuji ya rubuta ba ta da alaka da jam'iyyar NNPP kuma ba tare da sahalewarta ba ne."

Kara karanta wannan

Borno: Majalisar dattawa ta faɗi sakacin da ya jawo aka kai harin bam a Gwoza

"Kan maganar rigimar masarautu, lamarin yana gaban kotu kuma tsoma bakin Majalisar kawai kara ruruta wutar rikicin zai yi."

- Jam'iyyar NNPP

Jam'iyyar ta kara da cewa ta himmatu wurin tabbatar da kawo ci gaba a Najeriya da inganta rayuwar al'ummar kasar.

A yanzu dai akwai rigima a NNPP, kowane bangare yana ikirarin shi yake rike da jam'iyya.

Kungiya ta zargi Kwankwaso da rigimar masarautu

Kun ji cewa wata kungiya mai suna Progressives League of Youth Voters ta zargi Rabiu Kwankwaso da rubuta wasika ga ƴan Majalisa kan rigimar sarauta.

Ana zargin Sanatan ya rubuta takarda ne domin umartan mambobin NNPP su tasa Bola Tinubu a gaba kan zargi hannu a rigimar sarautar jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel