Zamfara: Matasan APC Sun Takawa Sanata Marafa Burki Bayan Farfado da Tsagin Jam’iyya
- Wasu matasa a jam'iyyar APC ta jihar Zamfara sun yi martani ga Sanata Kabiru Marafa kan yunkurin raba kan ƴaƴan jam'iyyar
- Matasan sun ce a yanzu Sanata Kabiru Marafa ba shi da wani tasiri a siyasar jihar Zamfara da zai jagoranci raba jam'iyyar gida biyu
- Rahotanni sun nuna cewa Sanata Marafa ya fara kokarin farfaɗo da tsagin jam'iyyar APC ne bayan an fara daina yi da shi a siyasance
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Wasu matasa yan kungiyar APC Youth Alliance a Zamfara sun takawa Kabiru Marafa burki kan farfaɗo da tsagin jam'iyya.
Matasan sun yi martani ne ga Sanata Kabiru Marafa bayan ya fara kokarin farfaɗo da tsagin jam'iyyar wanda zai kai ga raba kan ƴaƴanta.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban kungiyar, Tijjani Kaula Shinkafi ne ya yi martani ga Sanata Marafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kaula: 'Marafa ba zai yi tasiri ba'
Shugaban kungiyar APC Youth Alliance, Tijjani Kaula Shinkafi ya ce Sanata Marafa ba shi da wani tasiri a siyasar jihar Zamfara.
Saboda haka kungiyar ta buƙaci Sanata Marafa ya amice da cewa zamaninsa ya riga ya wuce a siyasar jihar.
Ko jama'a za su bi Sanata Marafa?
Tijjani Kaula Shinkafi ya ce al'ummar Zamfara ba za su bi Sanata Kabiru Marafa a sabon tsagin da ya kirkiro ba, rahoton Peoples Daily.
Ya kara da cewa ko da Sanata Marafa ya dage kan kafa tsagin jam'iyyar APC a Zamfara to sai dai ya yi tafiya shi kadai.
An zargi Marafa da saɓawa jami'yyar APC
Har ila yau, Kaula Shinkafi ya ce Sanata Marafa ya saɓawa tsarin shugabancin jam'iyyar APC wajen raba kan al'umma.
A karkashin haka ya ce ba zai samu goyon baya daga jami'yyar ba sai dai ya cigaba da zama shi kadai a gefe.
Limami ya ajiye aiki a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa babban malamin nan, Tukur Sani Jangebe ya sauka daga matsayinsa na yin limanci a masallacin Juma’a a jihar Zamfara.
Tukur Sani Jangebe ya bar kujerarsa ne saboda a samu zaman lafiya a masallacin kamar yadda ya sanar a wasikar yin murabus dinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng