Sarautar Kano: An Zargi Kwankwaso da Rubutawa ’Yan NNPP a Majalisa Wasika Kan Tinubu
- Kungiyar Progressive League of Youth Voters ta zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan yadda za a caccaki Bola Tinubu
- Kungiyar na zargin Kwankwaso da rubuta wasika ga 'yan Majalisa na NNPP kan korafi kan tsoma bakin Bola Tinubu a rigimar sarauta
- Jagoran kungiyar na kasa, Ambasada Abdul Usman Shaibu shi ya yi wannan zargi a jiya Litinin 1 ga watan Yulin 2024 a Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Wata kungiya ta zargi Sanata Rabiu Kwankwaso da neman hada kan 'yan Majalisar Tarayya na NNPP domin caccakar Bola Tinubu.
Kungiyar mai suna Progressive League of Youth Voters ta ce Kwankwaso ya dauki matakin ne kan zargin hannun Tinubu a rigimar masarautar jihar.
Sarautar Kano: Kungiya ta zargi Rabiu Kwankwaso
Shugaban kungiyar a Najeriya, Ambasada Abdul Usman Shaibu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Legit ta samu a jiya Litinin 1 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta zargi Kwankwaso ya rubuta takarda ga duka 'yan Majalisun NNPP domin kaddamar da shirin da zarar an dawo zaman Majalisar.
Shaibu ya ce Kwankwaso na zargin Tinubu da hannu dumu-dumu a rigimar masarautun jihar Kano ya ake ci ki a yanzu.
Ya ce an rubuta takardar a ranar 24 ga watan Yunin 2024 ga 'yan Majalisar NNPP a Tarayya da kuma na jihohi a cewar Pulse.
An zargi Kwankwaso da neman caccakar Tinubu
Kwadinetan ya ce Kwankwaso a cikin takardar ya bukaci mambobin su fara korafin a zaman Majalisar a Abuja kan zargin Tinubu da hannu a rigimar.
"Muna da tabbaci kan wasikar da Kwankwaso ya rubuta ga duka mambobin NNPP a Majalisar Tarayya."
"A cikin wasikar, Kwankwaso ya bukaci su yi amfani da ikonsu wurin matsawa Bola Tinubu da Gwamnatin Tarayya kan cire hannu a rigimar masarautun Kano."
"Ya kuma bukaci 'yan Majalisar su goyi bayan gwamnatin jihar Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf."
- Abdul Usman Shaibu
Kwankwaso ya maka EFCC a kotu
Kun ji cewa Babbar kotun jihar Kano za ta fara zaman sauraron ƙorafin da Rabiu Kwankwaso da wasu mutum bakwai suka shigar da EFCC.
Jagoran NNPP da sauran mutanen su bakwai sun maka hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC a gaban kotun ne kan abin da ya shafi tauye haƙƙinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng