Manyan Dalilai 3 da Za Su Iya Jawo Buhari Ya Goyi Bayan Takarar Atiku a Zaben 2027
Daura, Katsina - Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ziyarci Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina inda wasu ke ganin bai rasa nasaba da zaben 2027.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Duk da Atiku ya ce ya kai ziyarar domin taya Buhari murnar bikin babar sallah, amma wasu na ganin akwai siyasa a ziyarar da ya yi.
Atiku ya shafe shekaru 30 yana neman shugabancin Najeriya amma bai yi nasara ba inda ya fara tsayawa takara tun a shekarar 1993 da marigayi Moshood Abiola.
Legit Hausa ta zakulo muku dalilai uku da ake ganin ka iya saka Buhari goyon bayan Atiku a zaben 2027 da ke tafe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Hadakar 'yar Arewa
Ziyarar Atiku a kwanakin nan ga tsofaffin shugabannin Najeriya a Arewa zai iya zama shirin kwace mulkin Bola Tinubu a zaben 2027.
Atiku a cikin kwanakin nan ya ziyarci tsofaffin shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar da kuma Muhammadu Buhari.
Wadannan ziyarce-ziyarce cike suke da zargin kulle-kullen siyasa da ake shiryawa domin zaben 2027 da ke tafe.
2. Zargin Buhari da kashe kasa
Mukarraban Tinubu da dama sun sha zargin gwamnatin Buhari da jefa kasar a cikin mawuyacin hali da yanzu ake ciki.
Tsohon shugaban APC, Sanata Adams Oshiomole ya ce 'yan Najeriya na shan wahala ne saboda gurbatattun tsare-tsaren Buhari.
Sannan wasu 'yan siyasa daga APC da kungiyoyi har ma da Sarkin Kano, Sanusi II sun daura alhakin halin kunci a yanzu kan Buhari wanda hakan ba zai yi wa magoya bayansa dadi ba.
3. Korar wadanda Buhari ya nada
A watan Yunin 2023, Tinubu ya sallami dukkan hafsoshin tsaro da Buhari ya nada wanda hakan ke nuna bai aminta da kwarewarsu ba.
Sauran sun hada Godwin Emefiele na CBN da Abdulrasheed Bawa na EFCC da Babagana Monguno da kuma Lauretta Onochie.
Atiku ya fadi dalilin ziyartar Buhari
Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya fadi musabbabin ziyartar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Atiku ya ce ya kai ziyarar domin taya Buhari murnar kammala bukukuwan babbar sallah lafiya ba kamar yadda ake zaton akwai siyasa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng