“Za Ki Gane Shayi Ruwa Ne”: Ministan Tinubu Ya Sha Alwashin Kayar da Sanata a 2027

“Za Ki Gane Shayi Ruwa Ne”: Ministan Tinubu Ya Sha Alwashin Kayar da Sanata a 2027

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya fusata bayan Ireti Kingibe ta tube masa zani a kasuwa kan rashin katabus a ofis
  • Sanata Kingibe ta ce Wike bai tsinana komai ba kuma mutanen Abuja suna fushi da shi saboda ya lalata komai a birnin tarayyar
  • A martaninsa, Wike ya sha alwashin kayar da ita idan ta fito neman takara a 2027 inda ya ce yanzu shi ne yake mulkin Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sha alwashin hana sanatar Abuja dawowa Majalisar Dattawa a Najeriya.

Wike ya bayyana haka ne yayin martani bayan Sanata Ireti Kingibe ta ce 'yan Abuja ba su ganin aiki da Wike ke yi a birnin.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya fadi matakin da zai dauka kan Wike idan suka hadu nan gaba

Minsitan Tinubu ya sha alwashin kifar da Sanatar Abuja a zaben 2027
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi alkawarin kayar da Sanata Ireti Kingibe a birnin. Hoto: @IretiKingibe, @GovWike.
Asali: Twitter

Kingibe ta caccaki Wike kan rashin katabus

Sanata Kingibe ta caccaki Wike ne inda ta ce babu asibitoci da makarantu da kuma tsaftataccen ruwan sha a Abuja a hirarta da Arise TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin martaninsa, Wike ya ce ba ya shiga ofishin ba ne domin ya burge ta inda ya ce ya yi abin a zo a gani a watannin da ya yi a matsayin Minista.

Ministan ya ce a 2027 sanatar za ta gane shayi ruwa ne domin ko kusa ba za ta koma kujerarta a Majalisar Dattawa ba.

Ya ce abin takaici ne madadin ta hada kai da shi domin kawo cigaba amma tana jin haushi mutanen Abuja na yabon gwamnatin Bola Tinubu, cewar Daily Trust.

Wike ya sha alwashin kayar da Kingibe

"Na ji wata tana magana a gidan talabijin na Arise TV, abin takaici ne wai daga Majalisar Dattawa ta ke."

Kara karanta wannan

Fitaccen jarumin Nollywood, Olu Jacobs ya rigamu gidan gaskiya?

"Abin da mutum bai sani ba, bai sani ba, abin da kuma ya sani ya sani idan har baka sani ba ya kamata a koyar da kai."
"Cikin 'yan watannin da muka yi mai maganar tana jin haushi ana yabonmu, idan bai yi maki ba, ki je ki rungumi tIransifoma."
"Ina kalubalantar 'yar Majalisar, idan tana da jama'a ta fito a 2027 zamu kayar da ita, kina tunanin abin da ya faru a baya zai faru yanzu, ni ne MinIstan Abuja yanzu."

- Nyesom Wike

Shehu Sani zai kalubalanci Wike

Kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya yi martani kan maganar da Ministan Abuja Nyesom Wike ya fada a kansa yayin wani taro.

Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya kalubalanci Shehu Sani da ya nuna ayyukan cigaba da ya kawo a lokacin da yake Sanata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.