“NNPP Ta Barar da Damarta”: APC Ta Fadi Yadda Za Ta Kwace Mulkin Kano da Zamfara

“NNPP Ta Barar da Damarta”: APC Ta Fadi Yadda Za Ta Kwace Mulkin Kano da Zamfara

  • Jam'iyyar APC a Najeriya ta bayyana shirinta na kwace mulkin Kano da Zamfara ganin yadda suka rasa madafa
  • Sakataren yada labaran jam'iyyar a Arewa maso Yamma, Musa Mada shi ya tabbatar da haka inda ya ce sun shirya tsaf
  • Mada ya ce gwamnatin Kano kawai bata lokacinta ta ke tare da kawo tsare-tsaren da ba su da amfani ga al'umma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jam'iyyar APC ta bugi kirji kan shirin kwace mulkin NNPP a jihar Kano da kuma PDP a Zamfara a zaben 2027.

Jam'iyyar ta ce duba da yadda jihohin suke bata lokaci kan wasu tsare-tsare da ke rage musu farin jin a jihohinsu, za su yi musu bazata.

Kara karanta wannan

"Siyasa ce kawai": NNPP ta kalubalanci EFCC kan binciken Kwankwaso, ta nemi hujjoji

APC ta nemo hanyar kwace mulkin Kano da Zamfara a 2027
Jam'iyyar APC ta koka kan yadda ake gudanar da mulki a jihohin Kano da Zamfara. Hoto: Dr. Abdullahi Ganduje, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Yadda APC ta shirya kwace mulkin Kano

Sakataren yada labaran jam'iyyar ta kasa a Arewa maso Yamma, Musa Mailafiya Mada shi ya bayyana haka yayin hira da jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mada ya ce a Kano mutane suna nadamar zaben NNPP saboda ta buge da wasu tsare-tsare da ba su taimakon talakawa.

Ya ce a Zamfara kuwa, Dauda Lawal yana aiki ne ga jam'iyyar APC saboda a kan tsaro ya gina yakin neman zabe kuma bai tsinana komai ba.

"NNPP ta gaza yiwa al'umma aiki" - APC

"NNPP kawai tana bata lokaci ne, sun buge da shirme da bai da amfani ga jama'a da suka hada da rusau da kuma rusa masarautun jihar."
"APC tana yiwa gwamnatin Kano godiya saboda tana ba ta kofar kwace mulki cikin sauki, jama'a da dama ba su son abin da ke faruwa a jihar."

Kara karanta wannan

Sadiya Haruna ta tona asirin aurenta da G-Fresh, ta sha mamaki a daren farko

"Yan Kano suna nadamar zaben NNPP tun yanzu, za mu yi amfani da hakan domin kwace mulki amma ba da shi kadai muka dogara ba."

- Musa Mada

Mada ya ce suna da dama sosai a Kano ganin shugaban APC da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa duk 'yan Kano ne.

A jihar Zamfara kuwa, Mada ya ce Gwamna Dauda Lawal sai bata lokacinsa ya ke yi wurin aibata gwamnatin da ta shude madadin aiki ga al'umma.

NNPP ta kalubalnaci EFCC game da Kwanwkaso

Kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta yi martani kan ci gaba da binciken Rabiu Kwankwaso da hukumar EFCC ke yi a Najeriya.

Jam;iyyar ta kalubalanci hukumar da ta kawo hujjoji kan binciken idan har ba bita da kullin siyasa ba ne kan sanatan

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel