Ana Daf da Zabe, Kwankwaso Ya Damƙi Sababbin Tuba Kusan 2,000 Zuwa NNPP
- Aƙalla mambobin jam'iyyu 1,648 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP a jihar Edo a ranar Alhamis 27 ga watan Yunin 2024
- Dan takarar gwamnan jihar a NNPP, Fasto Azehme Azena shi ya karbi sabbin tuban yayin tattakin zaman lafiya a Benin City da ke jihar Edo
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar a watan Satumbar wannan shekara ta 2024 da muke cikin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo, jami'yyar NNPP ta karbi sabbin tuba daga wasu jam'iyyu.
Dan takarar gwamnan jihar, Fasto Azehme Azena shi ya karbi sabbin tuban yayin tattakin zaman lafiya a ranar Alhamis 27 ga watan Yunin 2024.
Edo: NNPP ta karbi sabbin tuba
Dakta Azehme shi ya tabbatar da haka a daren jiya Juma'a 28 ga watan Yunin 2024 a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aƙalla magoya baya 1,648 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP ana daf da gudanar da zaben.
Sabbin tuban an karbe su ne yayin tattakin a Benin City da ke jihar Edo wanda Fasto Azehme ya jagoranci bikin.
Dr. Azehme ya yi godiya ga dubban jama'a da suka fito goyon bayansa wanda ba a taba gani ba yayin tattakin.
Edo: Kwankwaso ya taya Azehme murna
Idan baku manta ba, a kwanakin baya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taya kwamitin zaben fidda gwanin jihar Edo murnar kammala zaben lafiya.
Sanatan ya ce nasarar Fasto Azemhe Azena abin murna ne ganin yadda jam’iyyar NNPP ta fitar da dan takara da ya dace.
Dan takarar NNPP ya janye daf da zabe
A wani labarin, kun ji cewa wani dan takarar gwamnan jihar Ondo a jam'iyyar NNPP ya janye daga neman takara.
Israel Ayeni ya janye ne domin samun maslaha bayan dawowar wani jigon APC jami'yyar ana daf da gudanar da zaben gwamna.
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnonin Edo da kuma Ondo nan da watanni kadan masu zuwa.
Asali: Legit.ng