Shugaban NNPP Ya Faɗi Matsayin Naɗin Aminu Ado da Sarakuna 4 a Mulkin Ganduje

Shugaban NNPP Ya Faɗi Matsayin Naɗin Aminu Ado da Sarakuna 4 a Mulkin Ganduje

  • Jam'iyyar NNPP ta yi ikirarin cewa sarakunan da tsohon gwamnan Kano Ganduje y naɗa ba su da banbanci da kwamishinoni
  • Shugaban NNPP na Kano ya ce Ganduje ya naɗa Aminu Aso Bayero da sarakuna huɗu ne domin su taimake shi ya kawo Kano a zaɓen 2023
  • A cewarsa, tun da Muhammadu Sanusi II ya bar karagar mulki babu wanda ya maye gurbinsa sai yanzu da Abba Kabir ya maido da shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - New Nigeria People’s Party (NNPP) ta ce tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa sarakuna biyar ne domin ya kai labari a zaɓen 2023.

Shugaban NNPP reshen jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana haka yayin hira da ƴan jarida a ofishinsa da ke Kano ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Gingima-gingiman lauyoyi sun soki hukuncin kotu, sun zargi ƴan siyasa

Ganduje da Abba Kabir.
NNPP ta yi ikirarin cewa sarakunan da Ganduje ya naɗa matsayinsu ɗaya da kwamishinoni Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Hashimu ya yi iƙirarin cewa Ganduje ya tarwatsa masarautar Kano zuwa gida biyar gami da naɗa Aminu Ado Bayero da sarakunan Gaya, Rano, Karaye da Bichi don cimma burin siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Ganduje na naɗa sarakuna 5

Kamar yadda Daily Trust ta kawo, shugaban NNPP ya ce naɗin sarakunan ba shi da banbanci da naɗin siyasa na kwamishinoni don ya samu nasara a 2023.

Ya ƙara da cewa sarakunan ɗaya suke da kwamishinonin Ganduje, yana mai ƙarawa da cewa su gode Allah sun ɗana mulki duk da ƙarewar wa'adin Ganduje.

A rahoton The Nation, Hashimu ya ce:

“Sarakunan guda biyar da muka zo muka taras, kwamishinoni ne kawai da Ganduje ya nada domin su taimaka masa ya ci zabe a 2023. Kuma ba su kai labari ba shiyasa wa'adinsu ya kare."

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Shehu Sani ya kawo hanyar warware rikicin masarautar Kano

"Kamata ya yi tun lokacin da Ganduje ya faɗi zaɓe su ma su bar muƙamansu saboda bayan tafiyar Muhammadu Sanusi II babu wanda ya maye gurbin sarkin Kano.
"Amma kila ba su yarda cewa wa’adinsu ya kare ba bayan da mai gidansu ya sha ƙasa a zaben 2023.

Shugaban jam'iyyar NNPP ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuɓe su daga matsayin sarakuna ne saboda ƙorafe-ƙorafen da jama'a suka yi cewa ba su da sarki a Kano.

Abba ya caccaki kafa tuta fadar Nassarawa

Kuna da labarin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana dalilin da ya sa aka ga tuta a ƙaramar fadar Nassarawa, wurin da Aminu Ado Bayero ke zaune

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tona ya ce fadar ta ɗaga tutar ne domin jawo hankalin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel