An Bayyana Lakanin Peter Obi Na Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2027
- Mataimakin shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa, ya yi martani kan kiraye-kirayen da ake yi na Peter Obi ya fice daga jam'iyyar
- Ayo Olorunfemi ya bayyana cewa magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasan a zaɓen 2023 na gaskiya ba za su ba shi wannan gurguwar shawarar ba
- Ya bayyana cewa a jam'iyyar ne kaɗai Peter Obi zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 kuma suna yin shiri a kan hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban jam’iyyar Labour Party (LP) na ƙasa, Ayo Olorunfemi, ya yi magana kan batun takarar Peter Obi a zaɓen 2027.
Ayo Olorunfemi ya bayyana cewa jam'iyyar ita ce ta fi dacewa Peter Obi ya yi takara a cikinta domin lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Ana hurowa Peter Obi wuta a LP
Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya fuskanci matsin lamba daga wasu magoya bayansa 'Obidients' da ya fice daga jam’iyyar kafin zaɓen 2027 saboda rikicin da ta faɗa a ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake martani kan kiraye-kirayen Peter Obi ya fice daga jam'iyyar a yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Laraba, Olorunfemi ya ce ƴan 'Obidients' na gaskiya ba za su ba shi wannan shawarar ba.
"Eh to zan yi amfani da kalmar cewa sun ruɗe ne, waɗanda suke waɗannan maganganun a ruɗe suke. Ƴan 'Obidients' na gaskiya ba za su ba Peter Obi shawarar ya bar jam'iyyar ba."
"Akwai ƴan 'Obidients' na gaskiya, ƙungiyoyin ɗalibai na Najeriya, jajirtattun ƴan Najeriya, duk sun gaji da abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan, mutane sun gaji da yunwa, wacce jam'iyya zai koma? Ya koma PDP, APC ko ina?"
"Wannan jam'iyya ce wacce ta ginu a kan aƙida, mu ƴan dimokuraɗiyya ne. Mutanen da suka kafa jam'iyyar nan ƴan dimokuraɗiyya ne kuma hakan yana cikin kundin tsarin mulkinta."
"Saboda haka a jam'iyyar Labour Party ne kaɗai Peter Obi zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, kuma muna yin shiri a kan hakan."
- Ayo Olorunfemi
Abin da zai mayar da Peter Obi zuwa PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Peter Obi a matsayin shugaban ƙasa a 2023, Akin Osuntokun, ya yi magana kan yiwuwar ɗan takarar ya koma jam'iyyar PDP.
Akin Osuntokun ya bayyana cewa Peter Obi zai koma jam'iyyar PDP ne kawai idan za a ba shi tikitin yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng