"Kungiyar Nadamar Tarayya da Tinubu": Ɗan PDP Ya Yi Shaguɓe ga El Rufai, Kwankwaso

"Kungiyar Nadamar Tarayya da Tinubu": Ɗan PDP Ya Yi Shaguɓe ga El Rufai, Kwankwaso

  • Wani ɗan-a-mutun Atiku Abubakar ya lissafo waɗanda kwata-kwata ba su jin dadin yadda ake gudanar da mulkin APC a kasar
  • Abdulaziz Abubakar ya ce wasu 'yan APC suna nadamar tarayya da Tinubu da suka haɗa da Nasir El-Rufai da Yahaya Bello
  • Jigon PDP ya ce El-Rufai ya assasa kungiyar sai Abdulaziz Yari babban darakta da kuma Rabiu Kwankwaso babban majibincinta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar PDP ya yi shagube ga wasu 'ya 'yan APC da ba su jin dadin abin da ke faruwa a Najeriya.

Abdul-aziz Abubakar ya lissafo Nasir El-Rufai da Yahaya Bello da Rabiu Kwankwaso wadanda suke kungiyar nadamar tarayya da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamma ya faɗi gaskiya kan shirin tsige Mai aAfarma Sarkin Musulmi a Najeriya

Jigon PDP ya yi shaguɓe ga El-Rufai, Kwankwaso da Yahaya Bello
Dan PDP ya fadi wadanda ba su jin dadin gwamnatin Bola Tinubu ciki har da Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai, Asiwaju Bola Tinubu, Yahaya Bello.
Asali: Facebook

'Dan PDP ya fadi mukamin El-Rufai, Kwankwaso

Ɗan PDP wanda ke goyon bayan Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Litinin 24 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce El-Rufai shi ne ma'assasin kungiyar yayin da Sanata Abdul'aziz Yari ya zama babban darakta sai Kwankwaso babban majibincin kungiyar.

Wannan na zuwa ne bayan rasa mukamin Minista da El-Rufai ya yi da kuma binciken tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

"Sauran wadanda ke cikin kungiyar" - Dan PDP

Sai kuma Kwankwaso wanda ke zargin Tinubu da kitsa duk wata rigima game da dawo da Aminu Ado Bayero a jihar Kano.

Jigon PDP ya lissafo sauran da suka haɗa da Aisha Binani a matsayin shugabar mata sai Yahaya Bello shugaban matasa da kuma Sanata Kabir Marafa mai magana da yawun kungiyar da sauransu.

Kara karanta wannan

Duk da ikirarin gidansa 1 tak, an gano El Rufai ya mallaki gidan $193,084 a Dubai

"Ministocin Tinubu marasa amfani" - Dan PDP

A wani labarin, kun ji kewa 'dan adawar kuma na hannun daman Atiku Abubakar ya shawarci Bola Tinubu ya kori wasu Ministoci.

Abdulaziz Abubakar ya ce daga cikinsu akwai Ministan tsaro, Bello Matawalle da Ministan makamashi, Adebayo Adelabu da sauransu.

Hakan ya biyo bayan yawan korafe-korafen da ake yi kan wasu Ministoci a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu inda aka bukaci ya sallame su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel