"Na Yi Kuka": Hadimin Buhari Ya Fadi Abin da Ya Faru da Tsohon Shugaban Ya Nemi Su Yi Aiki Tare

"Na Yi Kuka": Hadimin Buhari Ya Fadi Abin da Ya Faru da Tsohon Shugaban Ya Nemi Su Yi Aiki Tare

  • Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana jin dadi yayin aiki da shi daga 2015 zuwa 2023
  • Femi Adesina ya ce lokacin da Buhari ya bukaci su yi aiki tare ya yi kuka sosai kuma yana tunanin ya karba ne ko a'a
  • Adesina ya bayyana haka yayin karanta littafin da ya rubuta game da Buhari mai suna 'Working with Buhari' a jihar Oyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Tsohon hadimin Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya magantu kan yadda ya karbi mukami a gwamnati.

Adesina ya ce lokacin da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci su yi aiki tare ya yi kuka sosai.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

Yadda hadimin Buhari ya yi kuka bayan masa tayin muƙami
Tsohon hadimin Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya fadi yadda ya ji bayan yi masa tayin mukami. Hoto: Femi Adesina.
Asali: Facebook

Femi Adesina ya yabawa halin Buhari

Tsohon hadimin ya bayyana haka ne a yau Asabar 22 ga watan Yunin 2024 a Ibadan da ke jihar Oyo yayin karatun littafinsa 'Working with Buhari', cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce yaji wani iri a lokacin saboda zai bar babban editan jaridar The Sun zuwa wani layi da bai sani ba.

"Mene zan tarar a can? Idan ba na son aikin fa, ko ba na son barin aiki na?."
"Sai dai na yi latti, kuma ina son Buhari, kuma ina son yin aiki da shi matuka."

- Femi Adesina

Buhari: Musabbabin wallafa littafin Femi Adesina

Adesina ya ce ya dade yana tallata Buhari tun 2003, inda ya ce ana biyansa kudi wanda bai kai abin da ya ke samu kaso daya cikin uku ba a matsayin babban editan The Sun.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: Lauya ya fadawa Abba yadda zai kawo karshen rikicin sarautar Kano

Ya ce abin alfahari ne yin aiki tare da Buhari kuma ya buga littafin domin kawar da tunanin da ake yi kan tsohon shugaban kasar.

Atiku ya ziyarci Buhari a Daura

Kun ji cewa Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina..

Atiku yana tare da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a yayin ganawarsu da Buhari a gidansa inda wasu ke ganin ziyarar na da alaƙa da siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.